IQNA

Wata Mai Yawon Bude Ido Daga Ukraine Ta Karbi Muslunci A Turkiya

13:58 - May 26, 2012
Lambar Labari: 2334258
Bangaren siyasa da zamantakewa, wata mai yawon bude ido daga kasar Ukraine mai bin tafarkin addinin kiristanci ta karbi addinin muslunci a matsayin addini rayuwa a kasar Turkiya bayan da ta saurari kiran sallah a garin safran.
Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo cewa, wata mai yawon bude ido daga kasar Ukraine mai bin tafarkin addinin kiristanci ta karbi addinin muslunci a matsayin addini rayuwa a kasar Turkiya bayan da ta saurari kiran sallah a garin safran inda ta zabi sunanJamra ya zama sunata bayan musuluntarta.
A wani bayanin kuma na daban adadin masallatai ya karu da kashi 74 cikin dari a kasar Amurka kamar dai yadda wani rahoto ya nuna wanda kungiyar jama’at Iman ta watsa a yau da ke cewa wannan adadi ya karu ne a cikin shekaru goma da suka gabata har zuwa karshen shekara ta 2011.
A cikin shekara ta 2000 masallatan da suke fadin kasar amurka a cikin dukkanin jahohi hamsin na kasar adadin bai wuce 1209 ba, amma ya zuwa shekara ta dubu biyu da goma sha daya adadin ya karu kashi saba’in da hudu idan aka kwatanta da wancan adadin, in da ya kai masallatai 2106 a cikin jahohi hamsin na kasar.
A cikin wani bangare na wannan rahoto an yi ishara da cewa, mafi yawan matasa mabiya addinin muslunci mazauna kasar Amurka, sun yi amannar cewa manyan jami’an gwamnatin kasar suna tsananin gaba da addinin muslunci da koyarwarsa, amma hakan ba zai hana su ci gaba da gudanar da harkokinsu na muslunci ba.
A cikin irin wannan yanayi day adaga cikin majalisar shura ta musulmin Amurka ya ce duk da matsin lamabar baya-bayan nan, an karbi mabiya addinin muslunci a cikin al’ummar Amurka duk kuwa da cewa su ne marassa rinjaye a kasar idan aka kwatanta da mabiya addinin kirista.
1015947

captcha