IQNA

22:53 - May 26, 2012
Lambar Labari: 2334571

Ta'addancin 'Yan tawayen Syria Na Ta Kara Kamari A kan fararen Hula

Bangaren kasa da kasa, 'yan ta'adda a kasar Syria na ci gaba da kara zafa-zafa harin ta'addanci da suke kaiwa kan fararen hula da jami'an da makaman da suke samu daga kasashen Amurka da haramtacciyar kasar Isra'ila gami da Saudiyya da kuma kasar Qatar da ke kare manufofin turawa kai da fata.

Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na cewa 'yan ta'adda a kasar Syria na ci gaba da kara zafa-zafa harin ta'addanci da suke kaiwa kan fararen hula da jami'an da makaman da suke samu daga kasashen Amurka da haramtacciyar kasar Isra'ila gami da Saudiyya da kuma kasar Qatar da ke kare manufofin turawa kai da fata a hanlin yanzu a yankin gabas ta tsakiya.
Daruruwan 'yan bindiga na kasar Syria da ke samun goyon bayan kasashen turai da wasu gwamnatocin larabawa sun kai hari a yau kan garin Shaumariyya da ke cikin gundumar Homs, inda suka bude wuta irin na kan mai uwa da wabi kan fararen hula, inda suka kashe mutane 12 har lahira.
Mai aiko ma gidan talabijin din Al-alam rahotanni daga kasar Syria ya sheda cewa, wasu dag cikin mutanen garin na Shaumariyya da suka samu dammar gudu sun sheda masa, sama da 'yan ta'adda 200 ne dauke da muggan makamai suke ta yin harbe-harben kan gidajen jama'a, inda suka kashe mutane 12 tare da jikkata wasu da dama, haka nan kuma sun kona gidaje sama da 20 mallaki jama'a wadanda suka ki ba su goyon baya.
A jiya ma 'yan ta'addan na Syria sun kaddamar da wani farmaki kan mutanen yankin Al-haula da ke kusa da birnin Homs inda suka kashe kanan yara 25, bisa zargin cewa mahaifansu na goyon bayan shugaba Bashar Asad, shedun gani da ido sun ce 'yan ta'addan sun kone babban asibitin gwamnati da ke garin na Haula kurmus, tare da wasu ofisoshin jami'an tsaro da ke makwaftaka da asibitin.
Kasashen Amurka da Saudiyya gami da Qatar sun sanar a hukumance kan cewa ne dai suke baiwa 'yan bindigar Syria kudade da makaman da suke kaddamar da irin wadannan hare-haren da su.
1015303


captcha