Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na afriqinfos cewa, masu bore a kasar Masar sun kai hari kan babban ofishin dan takarar neman shugabancin kasar mai zaman kansa Ahmad Shafiq inda suka banka masa wuta suka kone dukkanin abubuwan da suke ciki kurmus a cikin fushi inda aka tarwatsa su bayan wani dan lokaci.
Masu zanga-zanga a kasar Masar sun banka wa helkwatar yakin neman zaben Ahmad Shafiq tsohon firayi ministan kasar a lokacin mulki Mubarak sannan kuma wanda aka ce shi ne ya zo na biyu a zaben shugaban kasar da aka gudanar a kwanakin baya don nuna rashin amincewarsu da sakamakon zaben.
Kamfanin dillancin labaran kasar Masar ya bayyana cewar masu zanga-zangar sun kutsa helkwatar ne inda suka cinna mata wuta, sai dai kuma tuni jami'an 'yan kwana-kwana suka kashe wutar kuma sun ce babu wani da ya rasa ransa a lokacin gobarar.
Dubun-dubatan mutane ne suka fito kan tituna a bangarori daban-daban na kasar don nuna rashin amincewarsu da sakamakon zaben da aka sanar a jiya litinin inda aka ce Ahmad Shafiq da dan takaran kungiyar Ikhwan Muhammad Mursi wanda ya zo na daya su ne za su fafata a zagaye na biyu na zaben.
Daya daga cikin 'yan takaran shugabancin kasar a zaben da aka gudanar din Khaled Ali ya shiga cikin zanga-zangar da ake yi a Dandalin Tahrir na birnin Alkahira yana mai cewa wajen ne aka kifar da gwamnatin Mubarak don haka wajibi ne ma wajen ya zamanto wajen da za a kawo karshen kokarin da Ahmad Shafiq wanda aka ce yana samun goyon bayan sojoji masu mulki a kasar yake yi na dawowa karagar mulki
1019344