IQNA

Mahukuntan Kasar Bahrain Sun Saki Mai Kare Hakkin Bil Adama Bisa Beli

13:57 - May 30, 2012
Lambar Labari: 2337813
Bangaren kasa da kasa, mahukuntan kasar Bahrain sun saki shugaban kungiyar kare hakkin bil adama ta kasar Nabil Rajab wanda suka gurfanar das hi a gaban kuliya ba tare da wani dalili na kama shi ba, lamarin day a fuskanci akkakusar suka daga kungiyoyin kare hakkin bil adama na duniya,
Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na tashar Al-alam cewa, mahukuntan kasar Bahrain sun saki shugaban kungiyar kare hakkin bil adama ta kasar Nabil Rajab wanda suka gurfanar das hi a gaban kuliya ba tare da wani dalili na kama shi ba, lamarin day a fuskanci akkakusar suka daga kungiyoyin kare hakkin bil adama na duniya da suka hada da kungiyar kare hakkin bil adama da majalisar dinkin duniya.
Dubban mutane ne suka gudanar da zanga-zanga a dukkanin yankunan kasar Bahrain, tare da kara jadda cewa babu gudu babu ja da baya kan neman sauyi a cikin harkokin mulki da siyasar kasar ta hanayar lumana, duk kuwa da matakan rashin imanin da mahukuntan kasar ke dauka a kansu.
Gidan talabijin din Al-alam ya bayar da rahoton da ke cewa, a daren jiya dubban mutane sun fantsama kan manyan titian a yankuna daban-daban na kasar da suka hada har da birnin Manama fadar mulkin kasar, inda suka yi ta rera taken neman ‘yanci, da kuma kira ga dakarun mamaya na masarautar Saudiyya da suke taimaka ma jami'an tsaron kasar wajen murkushe fararen hula masu zanga-zangar lumana, rahoton ya ce jami'an tsaro sun yi amfani da hayaki mai sanya hawaye da duka da kulake a kan masu zanga-zangar.
A cikin makon da ya gabata ne dai kwamitin kare hakkin bil adama na majalisar dinkin duniya ya gudanar da zama kan rikicin na Bahrain, tare da halartar kungiyoyin kare hakkin bil adama daga kasashen duniya da suka hada da Amnest International da kuma Human Rights Watch, inda suka dora alhakin cin zarafin dan adam da ake yi a kan masarautar kasar.
1019395
captcha