Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na jaridar Alwasat cewa, kafa tutar haramtacciyar kasar Isra’ila a gaban kubbatus shakra babbar barazana ce ga alamu na muslunci a yankin palastinu baki daya musamman a yankunan Qods wanda yahudawan sahyuiya suka mamaye tare da kokarin mayar da shi mallakin yahudawan sahyuniya masu kiyayya da addinin muslunci.
Jaridar ta fara ne da labarin da ke cewa, kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Syria Jihad Maqdisi ya karyata zargin da kasashen turai gami da ‘an adawar kasar suka yi kan dakarun gwamnatin kasar, dangane da kisan gillar da wasu mutane da ba asani ba suka yi fararen hula a kauyen Hulah da ke cikin gundumar Homs.
A wani taron manema labarai da ya gudanar jiya a birnin Damascus Jihad Maqdisi ya ce, bias bayan da suka samu daga mutanen kauyen, wasu mutane kimanin 200 ne dauke da muggan makamai suka shigo kauyen suna kabbara, kuma sun yi ta harbe-harbe da bindigogi irin na kan mai uwa da wabi, bayan da suka bar kauyen an samu gawawwaki dama a kan tituna da kuma cikin gidaje, da suka hada da na kananan yara sama da 30, kamar yadda suka jikkata mutane sama da 300.
Makdisi ya ce bababn rashin adalci kasashen turai su zargi gwamnatin Sria da hakan, domin kuwa sun san masu turo ‘yan ta’adda a cikin Syria da kuma bas u makamai da bama-bamai domin su kasha fararen hula da jami’an tsaro, ya ce gwamnatin Syria ta kafa kwamitin alkalai da masana harkokin tasro domin bincika lamarin, kuma kwamitin zai bayar da rahoto cikin kwanaki uku.
1019404