IQNA

Taron Kara Wa Juna Sani Kan gudunmawar Imam Khomeni (RA) Ga Musulmi A London

18:22 - June 02, 2012
Lambar Labari: 2339439
Bangaren kasa da kasa, ana shirin gudanar da wani zaman taro na karawa juna sani kan irin gudunmawar da marigayi Imam Khomeni Allah ya kara masa yarda ya bayar wajen ci gaban al’ummar musulmi da kuma fadakarta a wannan karni.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na bangaren hulda da jama’a na bababr cibiyar kula da harkokin musulunci cewa ana shirin gudanar da wani zaman taro na karawa juna sani kan irin gudunmawar da marigayi Imam Khomeni Allah ya kara masa yarda ya bayar wajen ci gaban al’ummar musulmi da kuma fadakarta a wannan karni da muke ciki.
A yayin wannan taro za a gabatar da jawabai wanda malamai da kuma masana gami da malaman jami’oi da maruta za su gabatar, inda za a yi bayani kan matsayinsa na ilimi da kuma irin gwagwarmayar da ya yi da manyan kasashen duniya ‘yan mulkin mallaka, wadanda suke danne sauran al’ummomin duniya tare da dora manufofin siyasarsu kan duniya bisa zalunci.
Yanzu haka dai ana shirin gudanar da wani zaman taro na karawa juna sani kan irin gudunmawar da marigayi Imam Khomeni Allah ya kara masa yarda ya bayar wajen ci gaban al’ummar musulmi da kuma fadakarta a wannan karni na dubu biyu.
1021426


captcha