Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo cewa, shugaban jam’iyyar Rasha demokradiyya ya sheda cewa bababr manufar taya da fitina acikin kasar Syria ita ce raunana kariyar da iran take da ita ta hanayawr kawancenta da gwamnatin Syria da suke baiwa gwagwarmayar palastinawa kariya da kuma ta Lebanon wanda ke bakantawa yammacin da karnukan farautarsu musamman ma daga cikin larabawa.
kungiyar alkaida ta ce ita ke da alhakin kai harin ta’addancin da ya yi sanadiyar mutuwar mutane da dama da sukahada da fararen hula da jami’an tsaro a kasar Syria da sunan jihadi a tafarkin Allah kamar yadda kungiyar wadda ta shahara da irin wadannan ayuka ta sheda lamarin da ya fuskanci gagarumar suka da Allawadai daga al’ummomin duniya.
A nasa bangare dan majlaisar dokokin kasar Lebanon daga gugun ‘yan majalisa na kungiyar hizbullah Nawwaf Musavi ya yi kira da a warware matsalar kasar Syria ta hanyar lumana maimakon kara zuzuta wutar rikicin da ake gani yanzu haka daga wasu kasashen larabawa.
Babban mai baiwa shugaban kasar Algeria shawarwari kan harkokin siyasa ya yi kakkausar suka kan kungiyar hadin kan kasashen larabawa dangane da matakin da ta dauka kan rikicin kasar Syria.
Jaridar Damas Post ta kasar Syria ta habarta cewa, a zantawar da ta yi da babban mai baiwa shugaban Algeria shawara kan harkokin siyasa Abdulaziz Bilkhaddam ya bayyana cewa, kungiyar hadin kan kasashen larabawa ta tafka babban kure dangane da matakin da ta auka kan rikicin kasar, inda take neman agaji daga kasashe makiyan larabawa da su taimaka mata domin kawo karshen gwamnatin Syria, y ace maimakon haka da ya kamata kungiyar kasashen larabawa ta taimaka wajen warware rikin ne ta hanyar dukkanin bangarori zuwa tattaunawa, ba goyon bayan 'yan adawar Syria da suke dauke da makamai ba.
Kungiyar kasashen larabawa tare da Amurka da Faransa da kuma Birtaniya har ma da haramtacciyar kasar Isra'ila ta bayan fage, sun hada kai domin ganin bayan shugaba Asad ko ta wace hanya, da hakan ya hada da baiwa 'yan bindigar kasar makamai da makudan kudade.
1022102