Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa a zantawar da ya yi da malamin jami’ar Switzerland John Clod Bast ya bayyana cewa, hankoron da haramtaccioyar kasar Isara’ila take na ganin cewa ta mamaye birnin Qods da dukaknin kaddarorin musulmi da mabiya addinin kirista da suke cikin wannan birnin mai alfara na daga cikin alamun da suyke nuni da kawo karshen haramtacciyar kasar yahudawan sahyuniya wadda ta zama bababr sankara ga al’ummomin duniya.
A bangare guda kuma an gudanar da wani zaman taro a birnin Gaza domin yin kira ga dukaknin al’ummomin musulmi da na larabawa da su mike domin kwato masallacin Qods mai alfarma daga mamayar yahudawan sahyuniya, duk kuwa da cewa shekara da shekaru ana yin wannan kira amma da sannu ya fara tasiri a cikin zukatan musulmi da larabawa da sauran al’ummomi masu lamiri.
Bayanin ya ci gaba da cewa wannan zaman taro ya samu halartar masana da malaman addinin muslunci daga sassa daban-daban na yankunan da ke cikin zirin Gaza, kamar yadda wasu daga cikin mahalartan suka gabatar da laccoci da makaloli dangane da halin da ake ciki a birnin Qods, inda dukaknin wurare masu alfarma da ke birnin da kewaye ke fuskantar barazanar rushewa daga yahudawan sahyuniya, da hakan ya hada da masallaci mai albarka.
Masana da malamai sun gudanar da wani zaman taro a birnin Gaza domin yin kira ga dukaknin al’ummomin musulmi da na larabawa da su mike domin kwato masallacin Qods mai alfarma daga mamayar yahudawan sahyuniya, domin kara fito da matsayin wannan birnin mai albarka a wajen mabiya addinin muslunci da kiristanci na duniya baki daya.
1021684