IQNA

19:43 - June 05, 2012
Lambar Labari: 2340652

Shirye Shirye Kan Matakan Tsaron Na Taron Shahadar Imam Kazim (AS) A Bagadaza

Bangaren kasa da kasa; an daukan matakan tsaro na kare lafiyar jama'a a daidai lokacin taron juyayin shahadar Imam Musa Kazim da za a gudanar a ranar ashirin da biyar ga watan Khurdad na shekara ta dubu daya da dari uku da tis'in hijira shamsiya .





Kamfanin dillancin labarai na ikna da ke kula da harkokin da suka shafi kur'ani a nan jamhuriyar mausulunci ta Iran ne ya watsa rahoton cewa: an daukan matakan tsaro na kare lafiyar jama'a a daidai lokacin taron juyayin shahadar Imam Musa Kazim da za a gudanar a ranar ashirin da biyar ga watan Khurdad na shekara ta dubu daya da dari uku da tis'in hijira shamsiya .Imam Musa bin Jafar wanda aka fi sani da lakabin Alkazim shi ne limami na bakwai daga cikin limama goma sha biyu da za su zo bayan rihlar ma'aikin Allah tsira da amincin Allah ya tabbata a gare shi da kuma alayan gidansa tsarkaka kuma daya daga cikin limaman shiriya wadanda duk wanda ya bi su ya tsira duniya da lahira wanda kuma ya saba masu ya hallaka duniya da lahira ,riko da tafarkinsu riko ne da addinin musulunci domin su ne haske abin haskakawa da yayae duk wani duhu na addini da na rayuwa da sauran lamura nay au da kullum .Imam Musa Alkazim daya daga cikin Uttaratl ma'aikin tsarkakakku wanda duk wanda ya hada su da kur'ani zai samu tsira duniya da lahira kamar yadda yake duk wanda ya saba masu das u da kur'ani zai tabe duniya da lahira ko shakka babu kamar yadda hadisai da dama daga ma'aikin Allah suka tabbatar da hakan kuma su ne abin koyi ga duk wani mai hankali da hangen nesa kuma su ne jirgin tsira kum amadogarar addini .Ima Kazim yana daga cikin tushen itaciyar tsira da daukaka kuma tushjen iliminsa ya samo asali ne daga Ma'aikin Allah domin daya ne daga cikin kofofin wahayi da imani kamar yadda yake ma'aji ne na ilimin Allah.

Shi dai imam Musa bin Jafar Alkazim an haife shi ne a karshen mulkin bani umayya a shekara ta 128 hijira kamariya da girma a daidai lokacin da fasadin bani ummaya yayi tsanani da galazawa gidan manzon Rahama da fakewa da sunan khalifofin manzo. Kuma ya rayuwa ne a farkon daular Abasiyawa da suma kamar dal=ular zaluncin da ta gab ace ta suka danne da zaluntar zuriyar ma'aikin Allah musamman limaman tsira da aminci .Ya rayu karkashin tarbiyar ma'aifinsa Imam Sadik (AS) inda ya samu tarbiya da ilmantar da su a makaranta ta ilimi da tsauran Allah da ta kafu karkashin koyarwar addinin musulunci da gina mutum karkashin kamala da ma'anawiya . Ya rayu karkashin khalifancin Safah da Mansur wanda yi wa ma'aifinsa kisan gilla a ranar ashirin da biyar ga watan Shawwal na shekara ta 148 kuma bayan kisan gillar da aka yi wa ma'aifinsa Imam Sadik (AS) ya karfi limamanci cikin yanayi mai muni da ban tsoran shi ma a yi masa kisan gilla saboda haka ne ma ma'aifinsa Imam Sadik (AS) kafin ya yi shahada ya tarbiyartar das hi don ci gaba da isar da sakon da ma'aikin Allah ya zo das hi da yada addinin musulunci da adalci a doran kasa a cikin yanayi na bakar siyasa khalifofin abasiyawa. Imam Musa Kazzim ya rayu ciki yanayi na takurawa da kuma gallazawa ba iyaka da tsare shi a gidan yari da haruna Rashid ya yi da kuma kokarin yi masa kisan gilla ba iyaka daga karshe suka aiwatar da abin da suka yi ta kokarin yi karkashin umarnin Khalifa Haruna Rashid.


1021446
captcha