Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo cewa, an kori wani malamin jami’a a kasar Turkiya saboda tilasta dalibansa mata cire hijabin muslunci wanda a loktan bayan ya kasance doka ce da ta haramta hakan amma daga bisani aka soke wannan doka amajalisar dokokin kasar wadda ta kwashe shekaru tana bin tsarin babu ruwansa da addini.
A jiya shugaban cibiyar kula da ayyukan addini a jamhuriyar muslunci ta Iran kuma wakilin jagoran juyin juya halin muslunci ya kai wata ziyara ga babban sakataren kungiyar gwagwarmaya ta hizbullah a kasar Lebanon Sayyid Hasan Nasrullah tare da tawagarsa dake rufa masa baya, daga cikinsu har da jakadan jahuriyar mulunci a kasar Lebanon.
Wannan ganawa ta tabo abubuwa da dama da suka hada da dangataka tsakanin kungiyar hizbullah da kuma kasar Iran, da yadda ake samun gagarumin ci gaba a dukaknin fuskoki tsakanin kasashen Iran da Lebanon, wanda hakan ke kara tabbatar da cewa kasashen biyu suna da mahanga guda da ta hada su, ita ce ‘yancin siyasa da kuma zama cikin fadaka da karfafa alaka a tsakaninsu.
Muhammad Muhammadi shugaban cibiyar kula da ayyukan addini a jamhuriyar muslunci ta Iran kuma wakilin jagoran juyin juya halin muslunci ya kai wata ziyara ga babban sakataren kungiyar gwagwarmaya ta hizbullah a kasar Lebanon Sayyid Hasan Nasrullah tare da tawagarsa, inda suka gana a gidansa da ke birnin
1023618