Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na NUN cewa gwamnatin kasar Syria ta rufe dukaknin hanyoyin da suke isa hubbaren sayyida Zainab amincin Allah ya tabbata a gare ta domin kauce ma harin ‘yan ta’adda kan masu gudanar da ayyukan ziyara a kasar daga cikin gida da kuma sauran kasashen musulmi.
Kasashen turai da dama da suka hada da ita kanta kasar Faransa sun matukar damuwa kan makomar wannan juyi da yake faruwa acikin kasashen larabawa a wannan loikaci, domin kuwa abokansu ne akasari aka kawar.
Majalisar mabiya addinin muslunci da ke nahiyar turai ta kiray mabiya addinin muslunci da suke cikin kasar Switzerland ad suka kafa wata babbar majalisar ta musulmin kasar, wadda za ta rika bin kadun hakkokinsu da kuma sanin dukaknin lamurransu da abin da ke kai da komowa dangane da su, musamman am acikin yanayi da musulmin kasar suke fuskantar barazana.
Babban kwamitin musulmin nahiyar turai ne ya yi wannan kira, bisa la’akari da cewa a halin yanzu gwamnatocin kasashen turai suna daukar matakai na takura musulmi ta hanyoyi da dama, wanda hakan ya sanya ala tilas musulmi duk inda suke a cikin kasashen nahiyar su mike domin kare hakkokinsu, musamman kasashe da musulmi suke da yawa kamar Switzerland Jamus da kuma Faransa gami da Birtaniya da sauransu. 1024973