IQNA

An Gudanar Da Shirin Bayar Da Horo Ga Masu Wa’azi Na Musulunci A Pakistan

17:06 - June 11, 2012
Lambar Labari: 2344467
Bangaren siyasa da zamantakewa, an gudanar da wani shiri na horar da masu wa’azi da fadakar da jama’a akasar pakistan domin sanin hanyoyin dasuka dace wurin aiwatr da hakan a birnin Pindad na kasar wanda ke cikin jahar Pinjab a jiya.
Kamafanin dilalncin labaran iqna ya hbarat cewa, ya nakalto daga bangaren yada labaransa na yankin Asia cewa an gudanar da wani shiri na horar da masu wa’azi da fadakar da jama’a akasar pakistan domin sanin hanyoyin dasuka dace wurin aiwatr da hakan a birnin Pindad na kasar wanda ke cikin jahar Pinjab a jiya tare da halartar malamai sama da dari biyu masu wa’azi a sassa daban-daban na kasar.
Masana da dama suka ganin a lokacin malaman addinin muslunci na hakika suke ci gaba da hankoron ganin an samu fahimtar juna tsakanin dukaknin al’ummomin duniya tare da zaman lafiya wasu daga cikin masu kiran kansu malaman addini a kasar Sudiyya suna fitar da fatawoyin halascin kai hari kan saura mutane da ba musulmi ba.
A cikin wanmnan makon ne wani mutum da ake kira mai bayar da fatawa na gwamnatin Saudiyya Abdulaziz Bin Abdullah Al-sheikh, ya fitar da wata fatawa daga mahangarsa ta akidar wahabiyanci da ke kafirta musulmi kansu wadanda ba su bin wannan tafarki na wahabiyanci, inda ya halasta kaddamar da kai hare-hare kan wuraren ibadar mabiya addinin kirista do,in neman tsokana da haddasa rikici tsakanin mabiya addinan biyu.
1026357

captcha