IQNA

17:31 - June 11, 2012
Lambar Labari: 2344484

Kungiyar Hadin Kan kasashen Musulmi Ta Yaba Da Matsayin Faransa Kan palastinu

Bnagaren kasa da kasa, kungiyar hadin kan kasashen musulmi ta yaba da matsayin kasar Faransa dangane da abubuwan da dama da suka danganci palastinu musamman kin amincewa da gina matsugunnan yahudawa ‘yan kaka gida da haramtacciyar kasar Isra’ila take yi a halin yanzu.

Kmafanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na OCI cewa, Ihsan Auglo shugaban kungiyar hadin kan kasashen musulmi ya yaba da matsayin kasar Faransa dangane da abubuwan da dama da suka danganci palastinu musamman kin amincewa da gina matsugunnan yahudawa ‘yan kaka gida da haramtacciyar kasar Isra’ila take yi a halin yanzu a yankunan palastinawa da ta mamaye da ke gabacin birnin Qods.
Kungiyar kare hakkin bil adama ta duniya Amnesty international ta yi kakkausar suka kan masarautar kasar Saudiyya ta gidan sarautar Al-saud da suke mulki a kasar kan danne hakkokin bil adama da suke yi a kasar musamman mabiya tafarkin iyalan gidan manzon Allah marassa rinjaye wadanda aka mayar da su saniyar ware a cikin harkokin kasar.
A wani batun kuma masana da dama sun amannar cewa ficewar dakarunnato daga kasar Libya shi ne kawai hanyar kawo karshen rikicin da kasar atke fama da shi tun bayan kisan gillar da suka yi wa tsohon jagoran kasar a lokacin da suka kaddamar da hari da sunan taimaka ma ‘yan tawaye wadanda daga bisani kuma suka gagare su.
Gwamnatocin kasashen lebanon da Libya sun cimma matasa dangane da makomar Imam Musa Sadr da abokan tafiyarsa biyu ta hanyar kafa wani kwamiti da zai bi kadun wannan batu da ya hada dukaknin bangarorin biyu.
1026326


captcha