Kmafanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na jaridar yaum sabi ta kasar Masar cewa, za a fara gudanar da wani zaman taron kara wa juna sani dangane da matsayin Masara farkon bayyanar addinin muslunci da kuma matsayinta a tarihi kamar yadda a zo a cikin kur’ani mai tsarki da kuma littafan tarihi na magabata kuma dalilan da suka tabbatar da hakan.
Kungiyar kare hakkokin bil adama Amnesty International ta duniya ta yi kaakusar suka cin zarafin dan adam da haramtacciyar kasar Isra’ila take yi a cikin yankunan palastinawa wanda hakan ya yi hannun riga da dukaknin dokoki na kasa da kasa baki daya, tare da neman a kawo karshen zaluncin da suke fuskanta.
Sojin haramtacciyar kasar Isra’ila na cikin yin shirin fuskantar masu zanga-zangar lumana domin ranar kasa inda za su tuna da masallacin Quds ami alfarma da kuma yin kira da a kawo ma al’ummar palastine dauki daga zalunci da suke fama da shi da yahudawan sahyuniya da suka mamaye musu kasa da yankuna, a zirin gaza da kuma gabar yamma da kogin Jordan.
Bayanin ya ci gaba da cewa dubban daruruwan palaesyinawa v acikin yankunan gabar yamma da kogin Jordan da kuma zirin Gaza suke cikin gudanar da zanga-zangar ranar kasa, domin nuna duniya cewa batun palastinu yana raye, a hankoron da wasu daga cikin munafukan kasashen larabawa suke yi na mayar da maganarsu a bun mantawa baki daya a cikin duniyar larabawa da ma duniya baki daya.
1025735