IQNA

13:49 - June 12, 2012
Lambar Labari: 2345208

Hanyar Yanto Palastinu Daga Mamayar Yahudawan sahyuniya Ita Ce Gwagwarmaya

Bangaren siyasa, shugaban kasar Iran ya jaddada cewa gwahgwarmaya da yahudawan sahyuniya it ace hanyar kwato dukaknin yankunan palastinawa da yahudawan sahynuiya suka mamaye tsawon shekaru tare da tabbatar da cewa al’ummomin duniya sun bayar da tasu gudunmawar kan hakan.


Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo cewa, Ahmadinejad shugaban kasar Iran ya jaddada cewa gwahgwarmaya da yahudawan sahyuniya it ace hanyar kwato dukaknin yankunan palastinawa da yahudawan sahynuiya suka mamaye tsawon shekaru tare da tabbatar da cewa al’ummomin duniya sun bayar da tasu gudunmawar kan hakan domin tabbatar da adalci.
Shugaban kasar Iran Dakta Mahmud Ahmadinejad ya bayyana cewar irin sauye-sauyen da ke faruwa a duniya wani lamari ne da ke nuni da cewa duniya ta kama hanyar tabbatuwar tsarin adalci.
Shugaban na Iran ya bayyana hakan ne a wata tattaunawa da ya yi da tashar talabijin din Fonix ta kasar China inda ya ce tsarin da ke mulki a duniya a halin yanzu tsari ne da ke cike da zalunci da babakere kuma shi ne ummul aba'isin din irin koma bayan da al'ummomin duniya suke fuskanta da kuma hana su hakkokinsu. Don haka ne ma shugaban na Iran ya ce al'ummomi za su tabbatar da wadannan hakkoki na su ne kawai matukar suka ci gaba da yunkuri da kokari wajen dawo da su.
Yayin da aka tambaye shi kan shirin nukiliyan zaman lafiya na kasar, shugaban na Iran cewa ya yi matsayar kasar Iran kan wannan lamarin dai a fili yake, dukkanin ayyukan nukiliyan Iran yana karkashin sanya idon hukumkar kula da makamashin nukiliya ta duniya. Shugaban ya ce matsala guda cikin wannan lamari shi ne yadda manyan kasashen duniya suka shigo da siyasa cikin lamarin.
1027190


captcha