Kamfanin dillnacin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na tashar talabijin din Al-alam cewa, rahotannin sun habarta cewa sama da mutane miliyan daya ne aka tabbatar da cewa sun halarci taron tunawa da zagayowar ranar shahadar Imam Musa Kazim (AS) a hubabrensa da ke birnin Bagadaza fadar mulkin kasar Iraki domin raya wadannan taruka masu albarka da aka saba gudanarwa.
A ckin makon da ya gabata ne dai wasu 'yan ta'ada suka tayar da wasu bama-bamai kan masu ziyartar wannan hubbare mai tsarki da nufin dasa tsoro da firgici a cikin zukatan masu gudanar da irin wadanna taruka, amma kuma taron da aka gudanar ya tabbatar da cewa masoya Imam Musa Kazim suna kishinsa, kuma ba za a taba raba su das hi ba amincin Allah ya tabbata a gare shi.
An tabbatar da cewa sama da mutane miliyan daya ne aka tabbatar da cewa sun halarci taron tunawa da zagayowar ranar shahadar Imam Musa Kazim (AS) a hubabrensa da ke birnin Bagadaza fadar mulkin kasar Iraki domin raya wadannan taruka masu albarka da ke Bagadaza.
1030316