Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo ic-el cewa, a jiya an gudanar da wani zaman taro na tunawa da shahadar Imam Musa Kazim (AS) a birnin London na kasar Birtaniya wanda cibiyar kula da harkokin musulunci ta kasar ta dauki nauyin shryawa da gudanarwa tare da halartar malamai da kuma masana daga ko’ina cikin fadin kasar.
Majalisar mabiya addinin muslunci a kasar Faransa za ta shigar da kara kan mutanen da suek nuna matuar adawa da addinin muslunci a kasar faransa saboda abin da suke yi na kokarin haddasa rikici da rashin fahimtar juna tsakanin mabiya addinin musulunci da sauran mabiya addainai da suke zaune a kasar.
Bayanin ya ci gaba da cewa kasar Faransa na daga cikin kasashen nahiyar turai da suka fi yawan musulmi, ta yadda adadinsu ya zama su ne na biyu ta fuskacin yawa a kasar bayan mabiya addinin kiristanci, amma kuma duk da haka har yanzu gwamnatin kasar ba ta amince da addinin musulunci a hkumance ba amatsayin daya daga cikin addinain kasar, duk kuwea da cewa ta amince da addinin yahudanci.
Shigar da kara kan mutanen da suke nuna matuar adawa da addinin muslunci a kasar faransa saboda abin da suke yi na kokarin haddasa rikici da rashin fahimtar juna tsakanin mabiya addinin musulunci da sauran mabiya addainai, yin hakan zai zama tamkar wani hannunka mai sanda ga sauran masu irin wannan akida asauran kasashen turai.
1031692