IQNA

21:59 - June 21, 2012
Lambar Labari: 2351512

Masar A kan Tafarkin Juyin Juya Hali Na Biyu Sakamakon Siyasar Sojin Kasar

Bangaren kasa da kasa, dubban daruruwan mutane ne suke ci ngaba da gudanar da gangami a dandalin Tahrir da ke tsakiyar birnin Alkahira na kasar Masar, domin nuna rashin amincewa da abin da suka kira yunkurin kawar zababbiyar gwamnati da sojojin kasar ke nufin yi, masu gangamin dai suna rera taken cewa za su ci gaba da juyin da suka fara wanda bai kammala ba.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya nakalto daga shafin sadarwa na tashar talabijin din Alalm cewa, sakamakon matakan da majalisar sojin kasar ta dauka na rushe majalisar dokoki da al'umma ta zaba, da kuma tabbatar wa kansu iko a kasar ko da kuwa an tabbatar da halastacciyar gwamnati da mutane suka zaba.

Yanzu haka dai al'ummar Masar sun kasa kunnuwa su ji sakamakon karshe na zaben shugabna kasa da aka gudanar a kasar zagaye na biyu, wanda magoya bayan kungiyar ikhwan suka ce dan takararsu Muhammad Mursi ne ya lashe zaben bayan da wakilansu suka sheda kirga dukkanin kuri'un da aka kada, yayin da magoya bayan abokin hamyarsa Ahmad Shafiq suke ikirarin dan takararsu ne ya lashe zaben.

Majalisar Dinkin Duniya ta bukaci sojoji da ke mulki a kasar Masar da su damka ragamar mulkin kasar a hannun wanda al'umma ta zaba domin dora kasar a kan turbar dimokuradiyya ba tare da yin shisshigin a cikin karfin ikon da dokokin kasar suka bai wa sabon shugaban kasar ba.

Mataimakin Babban Magatakarda na Majalisar ta dinkin duniya kan al'amurran da suka shafi siyasa Oscar Fernandez Taranco, ya bayyana a gaban taron Kwamitin Tsaron MDD cewa dole ne sojoji su mutunta kundin tsarin mulkin kasar da kuma zaben da al'ummar Masar ta yi ta hanyar mika ragamar mulkin a hannun wanda ya samu nasara a zaben da ya gabata.

A shekaranjiya litinin dai Majalisar Mulkin Sojan kasar ta Masar ta bayyana cewa ''sabon shugaban kasar da al'umma ta zaba ba ya da karfin iko a kan sojojin kasar, sannan kuma sojojin ne za su tafiyar da wani bangare na karfin da Majalisar Dokokin kasar ke da shi a kan zababben shugaban kasa'', wata alama da ke nuni da cewa sojoji na da niyyar yi wa dimokuradiyyar da ake neman shimfidawa a kasar
1033545




captcha