Bangaren kasa da kasa, tawagar farko ta Iraniyawa masu ziyara amasallacin masallacin manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da iyalan gidansa tsarkaka abirnin Madina mai alfarma sun ziyarci masallacin mabiya tafarkinn iyalan gidan manzo da suke a birnin.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo cewa tawagar farko ta Iraniyawa masu ziyara amasallacin masallacin manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da iyalan gidansa tsarkaka abirnin Madina mai alfarma sun ziyarci masallacin mabiya tafarkinn iyalan gidan manzo da suke a birnin kamar yadda shugaban tawagar ya sheda.
za a gudanar da wani zaman taro domin samar da fahimtar juna tsakanin mabiya ddinin muslunci da kuma mabiya addinin kiristanci da ma sauran addinai a birnin London na kasar Birtaniya tare da halartar malamai da masana daga sassa na kasar da ma wasu kasashen ketare.
Wannan zaman taro yana daya daga cikin muhimamn taruka da kungiyar bunkasa harkokin ilimi da al’adu na muslunci ke shirin shiryawa abirnin na London, kuma ya samu karbuwa daga mutane da dama da aka aike musu da goron gayyatar halartar taron, musamman ma masana da malaman addinin muslunci na kasar da kuma wasu kasashen musulmi da na larabawa.
1035248