IQNA

22:31 - June 25, 2012
Lambar Labari: 2354338

Babban Malamin Takijikistan Ya Yi Kira Zuwa Ga Yin Aiki Da Shari’ar Musulunci

Bangaren siyasa da zamantakewa, babban malamin addinin muslunci na kasar Tajikistan ya kirayi ‘yan kasar da suke zaune a cikin wasu kasashe da su yi kokari su aikata shari’ar muslunci a duk inda suke saboda hakan shi ne abin da ubangiji ya yi umurni da shi a kn dukkanin masu imani.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo cewa, babban malamin addinin muslunci na kasar Tajikistan ya kirayi ‘yan kasar da suke zaune a cikin wasu kasashe da su yi kokari su aikata shari’ar muslunci a duk inda suke saboda hakan shi ne abin da ubangiji ya yi umurni da shi a kn dukkanin masu imani a duk inda suka samu kansu.
Jagoran musulunci ya bayyana cewa a halin yanzu tarihin bil'adama yana fuskantar wani gagarumin sauyi mai girma ne, daga nan sai ya ce: Bil'adama dai sun gwada dukkanin akidu na abin duniya da suka hada da gurguzu, jari hujja, ‘yan kasanci da rashin yarda da Ubangiji, to amma a halin yanzu suna a wani sabon yanayi ne wanda babbar alamar hakan ita ce irin yadda al'ummomi suka koma ga Allah Madaukakin Sarki da kuma neman taimako daga wajen karfi maras karewa na Ubangiji da kuma dogaro da koyarwar Ubangiji.
Haka nan kuma yayin da ya ke ishara da irin yadda gungun ‘yan kama karya da kuma lalatattun yahudawan sahyoniya da sauran ma'abota girman kan duniya suke juya duniya yadda suke so, Jagoran cewa ya yi: Yunkurin al'ummomin wannan yankin wajen tinkarar lalatattun ‘yan kama-karya wani bangare ne na gwagwarmayar bil'adama da mulkin kama-karyar yahudawan sahyoniya, sannan kuma bayan wani yanayi mai girma na tarihi, bil'adama za su tsira da wannan kama-karya mai tsananin hatsari. Ko shakka babu wannan sauyi mai girma da ke faruwa tabbaci ne na alkawarin Ubangiji na ‘yantar da al'ummomi (daga mulkin ‘yan kama-karya) da kuma tabbatar da iko na koyarwar Ubangiji.
Har ila yau kuma yayin da ya ke magana kan irin mutanen da suke ganin ba za a iya samun nasara a kan wadannan cibiyoyin kama-karya na yahudawan sahyoniya na duniya ba, Ayatullah Khamenei cewa ya yi: A shekarun baya da dama ba su yarda da cewa muminan matasan kungiyar Hizbullah (ta kasar Labanon) za su iya samun nasara a kan sojojin haramtacciyar kasar Isra'ila ko kuma yiyuwar faduwar dagutun kasar Masar da kuma gagarumin sauyi mai ban mamaki da aka samu a kasashen arewacin Afirka ba, haka nan irin tsayin daka, nasarori da kuma ci gaban da Jamhuriyar Musulunci ta samu. To amma gagarumin karfi na Ubangiji ya bayyanar da kansa cikin irin wadannan nasarori da kuma sauyi mai ban mamaki da ya faru. 1036270
captcha