Bangaren siyasa, wani daya daga cikin fitattaun tsoffin sojin kasar Masar ya bayyana cewa majalisar sojin kasar ta yi abin day a zubar da mutuncinta a kasar musamman ga mutane wanda hakan ya sanya a halin yanzu bat a da wani matsayi na doka kuma dole ta janye ta bar mutane su yi mulki na demokradiyya.
Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafn sadarwa na yanar gizo cewa wani daya daga cikin fitattaun tsoffin sojin kasar Masar ya bayyana cewa majalisar sojin kasar ta yi abin day a zubar da mutuncinta a kasar musamman ga mutane wanda hakan ya sanya a halin yanzu bat a da wani matsayi na doka kuma dole ta janye ta bar mutane su yi mulki na demokradiyya kamar yadda mutane suke bukata.
Zababben shugaban kasar Masar Muhammad Morsi ya fara kokarin kafa sabuwar gwamnatin kasar wacce ya ce za ta hada da dukkanin bangarori na al'ummar kasar Masar din., a jiya litinin ne dai sabon shugaban kasar Masar din ya isa sabon ofishinsa da ke fadar shugaban kasar don fara gudanar da ayyukansa kwana guda bayan sanar da shi a matsayin wanda ya lashe shugaban kasar da aka gudanar alhali kuwa magoya bayansa suna ci gaba da zaman dirshan din da suke yi a dandalin Tahrir da ke birnin Alkahira a kokarin da suke yi na tilasta wa sojoji masu mulki a kasar na su mika dukkanin madafan iko ga sabon shugaban kasar.
Wani na kurkusa da shugaba Morsi ya shaida wa manema labarai cewa tuni ya fara darasin sunayen sabbin jami'an gwamnatin da zai kafa din wanda aka ce za ta kumshi bangarori daban-daban na al'ummar kasar musamman jam'iyyun da suka kulla kawanye da kungiyar ikhwan al-Muslimin, shugabanni da 'yan siyasa daban-daban na duniya suna ci gaba da aikewa da sakon taya murnarsu ga sabon shugaban na Masar.
1037717