IQNA

Haramtacciyar Kasar Isra’ila Na Cikin Damuwa Kan Sauyi A Gabas Ta Tsakiya

21:59 - June 27, 2012
Lambar Labari: 2356116
Bangaren kasa da kasa, haramtacciyar kasar Isra’ila na cikin wani yanayi na damuwa matuka dangane da irin abubuwan da suke faruwa na sauyi a cikin kasashen yankin gabas ta tsakiya wanda hakan ya jefa gwamnatin yahudawan sahyuniya cikin yanayi na tsoro da firgici.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo cewa, haramtacciyar kasar Isra’ila na cikin wani yanayi na damuwa matuka dangane da irin abubuwan da suke faruwa na sauyi a cikin kasashen yankin gabas ta tsakiya wanda hakan ya jefa gwamnatin yahudawan sahyuniya cikin yanayi na tsoro da firgici saboda ba ta san makomar lamarin ba.
Minista mai kula da harkokin addinin muslunci a kasar Philipines ya bukaci a kara fadada alaka da jamhuriyar muslunci ta Iran musamman ma a bangarorin da suka shafi karatun kur’ani mai tsarki ta yadda hakan zai taimaka musu matuka wajen kara habbaka lamurran kur’ani mai tsarki a kasar tasu wadda adadin musulmi ke ci gaba da karuwa acikinta.
shugaban kwamitin amintattu na majalisar malaman kasar Bahrain Ahmad Zain ya sheda cewa shigar da sojojin mamayar kasar saudiyya suka yia acikin kasar Bahrain domin murkushe fararen hula masu zanga-zangar lumana da neman hakkokinsu da aka haramta musu ya yi hannun riga da dukaknin dokokin kasa da kasa, da ma dokokin kasar ta Bahrain.
A bangare guda kuma kungiyar kare hakkin bil'adama ta kasa da kasa Amnesty International ta bukaci a gudanar da bincike akan kisan da jami'an tsaro su ka yi wa wani mai zanga-zanga a gabacin saudiyya, a wani bayani da kungiyar ta kare hakkin bil'adama ta fitar ta bukaci a yi bincike mai zaman kanshi akan kisan da aka yi wa Isam Muhammad Abu Abdullah a lokacin da ya ke cikin zanga-zanga a garin Awamiyyah da ke gabacin kasar.
1038542
captcha