IQNA

Gwamnatin Jordan Ta Yi Gargadin Keta Alfarmar Masallacin Qods Mai Alfarma

21:59 - June 27, 2012
Lambar Labari: 2356120
Bangaren kasa da kasa, ministan kula da harkokin addinin muslunci na kasar Jordan ya yi gargadi ga haramtacciyar kasar kan ci gaba da keta alfarmar masallacin Qods mai alfarma da sauran wurare masu tsarki datake yi.
Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yar gizo na CPI cewa, ministan kula da harkokin addinin muslunci na kasar Jordan ya yi gargadi ga haramtacciyar kasar kan ci gaba da keta alfarmar masallacin Qods mai alfarma da sauran wurare masu tsarki datake yi musamamn a cikin lokutan nan.
Daga cikin muhimman abubuwan da sabon kundin tsarin mulkin na kasar Syria ya kunsa, har da dokar kayyade wa'adin shugabancin kasar a cikin shekaru bakwai, kuma za a iya zabar shugaba a wa'ai na biyu, amma daga nan ba zai sake yin shugabanci a kasar ba.
Sa'anan kuma al'umma ne za su zabi shugaban kasa da kansu, maimakon zaben shi a majlaisar dokoki, kamar yadda sabon kundin tsarin mulkin ya bayar da damar kafa jam'iyun siyasa ba tare da wani haddi ba, kuma babu wani fifiko ga wata jam'iyya a kan wata. Haka nan kuma shugaban kasa dole addininsa ya zama muslunci, amma bisa sharadin zai girmama sauran addinai da ke kasar naki daya ba tare da nuna banbanci a tsakanin mabiyansu ba.
A wani bangare na sabon kundin tsarin tsarin mulkin kasar, ya bayar da 'yancin bude kafofin sadarwa masu cin gishin kansu, da kuma damar gudanar da taruka na siyasa da 'yancin bayyana ra'ayi, haka nan kuma bangaren shari'ar kasar zai kasance mai zaman kansa, tare da shiga kafar wando daya da duk wanda ya aikata laifi komai matsayinsa, da kuma yakar cin hanci da rashawa a dukaknin bangarorin gwamnati, da ma tsakanin jamaa'a, kamar yadda hukumar zabe za ta kasance mai cikakken iko da cin gishin kanta, ba tare da karbar umurni daga wani bangare da ke cikin siyasar kasar ba, da ma dai sauran batutuwa da dama da sabon kundin tsarin mulkin ya kunsa.
Masu bin digging lamurran da ke kai da komowa sun amannar cewa, idan al'ummar kasar Syria suka amince da wannan sabon kundin tsarin mulki, kuma aka samu damar aiwatar da dukaknin abin da ya kunsa, to hakan zai mayar da kasar abin koyi ta fuskacin demokradiyya ga sauran kasashen larabawan yankin gabas ta tsakiya, wadanda akasarinsu ba su taba sanin wani abu demokradiyya a cikin kasashensu ba, inda sarki ne wuka da nama a cikin dukaknin harkokin mulki da siyasa.
1038716


captcha