Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo cewa, dubban mutane ne akasarinsu magoya bayan kungiyar Ikhwanul musulmin a birnin Alkahira na kasar Masar suka gudanar da babban gangami a dandalin Tahrir da ke tsakiyar birnin na Alkahira domin nuna rashin amincewa da hankoron sojojin kasar na zarcewa kan mulkin kasar.
Zababben shugaban kasar Masar Mhd Morsi ya dauki alkawalin yin aiki tukuru domin ciyar da kasar da kuma al'ummarta gaba, wannan kuwa ba tare da nuna bambanci tsakanin wadanda suka jefa masa kuri'a da kuma wadanda suka zabi waninsa a lokacin zaben shugabancin kasar da ya gabata ba.
Mhd Morsi wanda yake gabatar da jawabi a gaban dubban mutane da suka taru a Dalilin Tahrir inda a can ne aka kaddamar da boren da ya yi sanadiyyar faduwar gwamnatin dan kama karya na kasar Hosni Mubarak, ya ce yana da cikakkiyar masaniya dangane da muhimman bukatun al'ummar kasar, musamman ma batun samar da ayyukan yi, inganta ilimi, kiwon lafiya, farfado da masana'antun kasar da dai sauran bangarori na ci gaban kasar.
Shugaban ya ce har abada ba zai taba mantawa da irin gagarumar rawar da al'ummar kasar suka taka wajen ganin cewa an dora kasar a kan kyakkyawar turba ta dimokuradiyya ba, to sai dai ya ce har yanzu akwai gagarumin aiki a gaban al'ummar kasar wajen ganin sun kare wannan nasara da suka sama, yana mai cewa duk wani kokari na tursasawa daga ciki ko kuma wajen kasar ba zai sa ya yi kasa a gwiwa wajen kare bukatun al'ummar kasar ta Masar ba.
A gobe dai ne aka shirya rantsar da Mhd Morsi a matsayin zababbiyan shugaban Masar na farko bayan juyin juya halin kasar.
1040482