Bangaren kasa da kasa, al’ummomin dunbiya da dama sun nuna matukar bukatuwa zuwa ga tsarin shariar addinin muslunci domin ya zama shi ne ke tafiyar da kasashensu a siyasance domin tababtar da cewa mutane suna bin sahahin tafarki na addini kamar yadda Allah madaukakin sarki ya yi umurni.
an raba wasu kwafofin kur’ani mai tsarki ga al’ummar palastinu mazauna yankin zirin Gaza wanda babbar cibiyar nan ta addini da ke kula da harkokin kur’ani a kasar Jordan ta kiyaye kur’ani ta taimaka wajen aiwatar da shirin kamar yadda ya gudana.
A bangare guda kuma Isma’il Haniyya pira ministan palastinu a yuankin Gaza ya bayyana cewa al’ummar palastinu suna gab da samun nasarar kwato masallacin Qods baki daya daga danniyar yahudawan sahyuniya wadanda suke hankoron rusa shi da kuma kawar da sauran dukaknin alamomi na musulmi baki daya.
Ya kuma byayana hakan ne a lokacin da yake gabatar da jawabi ga al’ummar kasar Tunisia a ziyarar da yake gudanarwa a wasui daga cikin kasashen yankin da suka hada Masar da kuma Suda gami da Turkiya, inda yake jadda matsayin kungiyar gwagwarmaya ta Hamas wajen ci gaba da yin gwagwarmaya domin samun ‘yancin al’ummar yankin na zirin Gaza.
Isma’il Haniyya ya bayyana cewa, yankin gabas ta tsakiya ya zama wani wurin buga misali da gwagwarmayar neman ‘yanci da fita daga karshin mulkin zalunci da kama karya azzaluman shugabanninsu da suke azurta kansu da dukiyoyin da al’ummar kasar suke da su. 1039555