IQNA

Gasar Karatun Kur’ani Mai Tsarki ta Daliban Jami’a Na Da Gagarumin Muhimmanci

20:14 - July 02, 2012
Lambar Labari: 2359460
Bangaren kur’ani, gudanar da gasar karatu da hardar kur’ani mai tsarki na daliban jami’a na kasashen musulmi na da gagarumin tasiri wajen kara fadada abin da ayoyinsa suke koyar da mu domin yin ko yi da su wanda kuma hakan yana da muhimmanci ga matasa musamman daliban jami’a su zama a sahun gaba wajen samun wannan matsayi.

Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo cewa, daya daga cikin makaranta kur’ani na kasa da kasa Mahmud Lotfi Niya ya bayyana cewa gudanar da gasar karatu da hardar kur’ani mai tsarki na daliban jami’a na kasashen musulmi na da gagarumin tasiri wajen kara fadada abin da ayoyinsa suke koyar da mu domin yin ko yi da su wanda kuma hakan yana da muhimmanci ga matasa musamman daliban jami’a su zama a sahun gaba wajen samun wannan matsayi a wajen Allah madaukakin sarki.
A cikin makon da ya gabata ne dai aka kammala gasar karatu da hardar kur’ani mai tsarki ta duniya a birnin Tehran fadar mulkin Jamhuriyar muslunci ta Iran tare da halartar wakilan kasashe daban-daban, musamman na musulmi da kuma na larabawa, inda aka samu halartar kasashe sama da hamsin, kuma an bayar da kyuatuka ga wadanda suka nuna kwazo.
gudanar da gasar karatu da hardar kur’ani mai tsarki na daliban jami’a na kasashen musulmi na da gagarumin tasiri wajen kara fadada abin da ayoyinsa suke koyar da mu domin yin ko yi da su wanda kuma hakan yana da muhimmanci ga matasa musamman daliban jami’a su zama a sahun gaba wajen samun wannan matsayi madaukaki. 1041962
captcha