Bangaren kur’ani, gasar karatu da hardar kur’ani mai tsarki da ake gudanarwa a matsayi na kasa da kasa daga kasashen duniya a kasar Iran tsawon shekaru ashirin da tara da suka gabata na daga cikin irinta masu matukar muhimmanci da suka birge mahalrta daga kasasne duniya duniya.
A zanatawar da ya yi da kamfanin dillancin labaran iqna Hasan Farahani dalibin jami’a na kasar Irabn da ya zo na daya a gasar, ya bayyana cewa gasar karatu da hardar kur’ani mai tsarki da ake gudanarwa a matsayi na kasa da kasa daga kasashen duniya a kasar Iran tsawon shekaru ashirin da tara da suka gabata na daga cikin irinta masu matukar muhimmanci da suka birge mahalrta daga kasashen duniya daban-daban.
A ci gaba da mayar da martanin da malaman addinin muslunci gami da masana suke yi kan malamin gwamnatin Qatar Yusuf Kardawi, ministan mai kula da harkokin addinin muslunci a palastinu Muhmud Habbash ya bayyana cewa fatawar da Yusuf Kardawi ya bayar da ke hana sauran musulmi ziyartar masallacin Qods mai alfarma ta sabawa koyarwar alkur’ani mai tsarki da kuma sunanr manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da iyalan gidansa tsarkaka.
A kwanakin baya ne Yusuf Kardawi da ake kallonsa amtsayin daya daga cikin mamalan duniyar sunna, kuma daya daga cikin malaman da suka taka rawa a baya domin ganin sun wayar da kan muslulmi kan babbar barazanar da ke tattare da kulla alaka da musulmi suke yi da haramtacciyar kasar Isra’ila, amma a halin yanzu ya zama malamin fadar sarkin Qatar, inda yake bayar da fatawowyi da suka yi daidai da abin da sarkin kasar ke bukatar ji, kasantuwarsa daya daga cikin karnukan farautar yahudawa.
1041882