IQNA

An Zabi Amin Pouya A Matsayin Wakilin Iran A Gasar kasa Da Kasa A Malazia

12:34 - July 04, 2012
Lambar Labari: 2360961
Bangaren kur’ani, an zabi Amin Pouya a matsayin wakilin Iran a gasar karatu da hardar kur’ani mai tsarki ta kasa da kasa da ake gudanarwa a birnin Kualalampour fadar mulkin kasar Malazia wanda zai gudanar da karatu a matsayi na duniya tare da ba shi damar shgiga cikin bangarorin gasar wadda za a gudanar a karo na hamsin da biyar.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo cewa, an zabi Amin Pouya a matsayin wakilin Iran a gasar karatu da hardar kur’ani mai tsarki ta kasa da kasa da ake gudanarwa a birnin Kualalampour fadar mulkin kasar Malazia wanda zai gudanar da karatu a matsayi na duniya tare da ba shi damar shgiga cikin bangarorin gasar wadda za a gudanar a karo na hamsin da biyar tare da halartar makaranta da mahardata na kasa da kasa.
Shugaban Majalisar Koli ta Tsaron kasar Iran Sa'ed Jalili ya ce babbar manufar kasashen Yammacin Turai da Amurka ita ce haddasa sabani a tsakanin kasashen Yankin Gabas ta Tsakiya domin cimma manufofinsu na siyasa da kuma na tattalin arziki a yankin.
Sa'ed Jalili ya bayyana hakan ne a Yammacin jiya lokacin da yake ganawa da shugaban Kungiyar Gwagwarmayar Samar da Sauyi ta Kurdawan kasar Iraki Naw-shirwan Mustafa Amin wanda ke gudanar da ziyara a nan birnin Tehran, inda ya ce matukar dai akwai cikakkiyar hulda tsakanin kasashen Iran da kuma Iraki, to lalle kuwa hakan zai karfafa hadin kai a tsakanin kasashen yankin Gabs ta Tsakiya ne baki dayansa.
Shugaban Majalisar ta Koli ya ce kasashen Yamma ke yayata farfagandar cewa akwai wani bambanci tsakanin Larabawa da Kurdawa kamar dai yadda suke cewa akwai wata kiyayya tsakanin musulmi 'Yan Sunna da kuma 'Yan Shi'a alhali kuwa a zahiri ba irin wadannan matsaloli tsakanin wadannan al'ummomi. Shi dai shugaban kungiyar ta Kurdawa Mustafa Amin ya ce Iran da Iraki kasashen ne masu matukar muhimmanci a wannan yanki, saboda haka hadin-kansu wani babban ci gaba ne ga al'ummar yankin.
1043841

captcha