Bangaren kur’ani, gasar kur’ani mai tsarki a kone lokaci ya kamata ta kasance tana isar da sakon kur’ani ne ga sauran mutane da suke sauraro musulmi da wadanda ba musulmi ba ta zama wani abun ado ba da kawata wuri domin kuwa manufa dai ita ce tunar da mutane sakon kur’ani mai tsarki.
Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo cewa, gasar kur’ani mai tsarki a kone lokaci ya kamata ta kasance tana isar da sakon kur’ani ne ga sauran mutane da suke sauraro musulmi da wadanda ba musulmi ba ta zama wani abun ado ba da kawata wuri domin kuwa manufa dai ita ce tunar da mutane sakon kur’ani mai tsarki.
Kasar Amurka da kuma kungiyar tarayyar Turai dole ne su dauki alhakin tabarbarewar tattalin arzikin duniya sanadiyyar takunkumin sayan danyen man kasar Iran da suka yi, Kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Iran Ramin Mehmanparas ne ya bayyana haka a yau litinin kwana guda bayan da kungiyar kasashen turai EU ta fara aiwatar da shirin dakatar da sayan danyen man kasar Iran a jiya lahadi.
Mehman paras ya ce takunkumin bangare guda na kasashen yamma zai samar da gibi mai yawa a cikin kasuwar makashi a duniya wanda kuma tabbas zai shafi makomar tattalin arzikin kasashen duniya gaba daya, Kakakin ya kara da cewa takunkumi sayan danyen man kasar Iran wanda kasashen yamma suka dorawa kasar Iran ya nuna a fili cewa wadannan kasashen basa mutunta kokarin da kasar Iran take yi na shiga tattaunawa da su a gungun kasashe 5+1 da kuma sauran kungiyoyi na kasa da kasa.
Daga karshe yace wannan takunkumin ba zai taba sanya kasar Iran ta yi watsi da hakkinta na sarrafa makamacin nuclear ta zaman lafiya ba kamar yadda takunkuma da suka gabata suka kasa yin hakan daidai da yarjeniyoyi na kasa da kasa.
1043415