IQNA

An Kira Ga Masu Gasar Kur’ani Da Isar Da Sakon Jamhuriyar Musulunci Ga Sauran Al’ummomi

17:20 - July 05, 2012
Lambar Labari: 2361551
Bangaren kur’ani, an yi kira ga masu halaratar taruka na gasar karatu da hardar kur’ani na kasa da kasa da ake gudanarwa a jamhuriyar muslunci da su yi amfani da wannan damar wajen isar da sakon juyin juya hali ga sauran al’ummomi na duniya domin samun ci gaba da bazuwar tunani na yanci da yantuwa daga ‘yan mulkin mallaka.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga hafin kula da rkokin gasar kur’ani ta duniya cewa, an yi kira ga masu halaratar taruka na gasar karatu da hardar kur’ani na kasa da kasa da ake gudanarwa a jamhuriyar muslunci da su yi amfani da wannan damar wajen isar da sakon juyin juya hali ga sauran al’ummomi na duniya domin samun ci gaba da bazuwar tunani na yanci da yantuwa daga ‘yan mulkin mallaka da suke hankoron danne sauran al’ummomi.
Kwamandan dakarun sama na dakarun kare juyin juya halin Musulunci na kasar Iran Birgediya Janar Amir Ali Hajizadeh ya bayyana cewar a duk lokacin da wani rikici ya taso to kuwa makamai masu linzami na dakarun kare juyin za su zamanto tamkar tsawa a kan makiya.
Janar Hajizadeh ya bayyana hakan ne a yau laraba jin kadan bayan kammala atisayen soji da dakarun kare juyin suka gudanar da aka ba shi sunan 'Atisayen Rasulul A'azam na 7 inda ya bayyana cewar ko da wasa al'ummar iran ba za su mika wuya ga barazanar makiya ba, sannan kuma za su mayar da martani ga duk wata barazana da dukkan karfinsu.
Kwamandan ya kara da cewa a yayin wannan atisayen dakarun kare juyin juya halin Musulunci na Iran din sun gwada nau'oi daban-daban na makamai masu linzami wanda hakan yake nuni da rashin yin tasirin takunkumin da aka sanya wa kasar Iran.
A ranar litinin din da ta gabata ne aka fara wannan atisaye na Rasulul A'azam na 7 sannan kuma a yau laraba ne aka kawo karshensa.

1044356

captcha