Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo cewa gwamnatin kasar Rasha tayi kakkausar dangane da irin matakan da kasashen yammacin turai suke dauka na nuna tsananin kiyayya da gaba ga shugaban kasar Syria Bashar Asad saboda manufofi na siyasa wanda hakan ya hada taimaka ma ‘yan ta’adda da suke kiran kansu masu neman sauyi ta hanayar tashin hankali.
Gwamnatin kasar rasha ta kirayi ‘yan adawar Syria zuwa ga hadin kai domin samar da zaman lafiya mai dorewa a kasar Syria ta hanyar zama kan teburin tattaunawa tare da gwamnatin kasar tare da yin watsi da ayyukan tashin hankali.
Ministan harkokin wajen kasar Rasha Sergey Lavrov ya bayyana hakan, inda ya ce gwamnatin Rasha tana yin iyakacin kokarinta domin ganin ta hada kan ‘yan adawar Syria domin su koma kan teburin tatatunawa tare da gwamnatin kasar ta Syria, domin samun hanyar warware rikicin kasar ta hanyar lumana da fahimtar juna, domin a cewarsa idan ba ta wannan hanya ba babu ranar da rikicin zai kawo karshe.
Sergey Lavrov ya karyata kalaman da suke fitowa daga bakunan jami’an gwamnatocin Amurka da na Birtaniya, da ke cewa Rasha ta amince Bashar asad ya safka daga mulki kamar yadda Amurka da sauran kasashen yammacin turai suke yi kira, ya ce wannan ba da daga cikin abin da aka cimma yarjejeniya a kansa zaman taro na Jenava.
A bangare guda kuma Lavrov din ya jaddada cewa Rash aba za ta halarci taron Amurka da kawayenta kan Syria ba, wanda za a gudanar a birnin Paris na kasar Faransa, a nata bangaren gwamnatin kasar China ta sanar yau Alhamis cewa ita ko alama ba za ta halarci wanann taro ba.
1044709