Kamfanin dillancin labarai na Ikna da ke kula da harkokin da suka shafi Kur'ani mai tsarki a nan jamhuriyar musulunci ta Iran ne ya watsa rahoton cewa; Barnad Henry Love bayahude mai akidar sahayoniuya da ke zaune a kasar Faransa wanda yak e da ra'ayin kisan gilla kan Palasdinawa wani nauyi ne na yaki da ta'addanci ya bayyana cewa: babban buri a rayuwarsa shi ne yahudanawa su rubuta kur'ani da yi masa gyara.Wannan bas hi ne karon farko da yake maganganu na takalar fada da neman tada hankali da fitina a tsakanin musulmi da yahudawa musamman idan aka yi la'akari da yadda ya yi fice da akidarsa ta yahudanci da bakar nuna adawa kan musulmi da addinin musulunci da kuma goyan bayan day a ke samu a fili karara .Kuma wannan akidarsa ta yi nuni da bayyana ta a fili duk da cewa shi bayahude ne haifaffen kasar Aljeriya a shekara ta dubu daya da dari tara da arba'in da takwas n=miladiya kuma uwayensa sun yi gudun hijira zuwa kasar Marokko a shekara ta dubu daya da dari tara da hamsin da hudu da zarcewa zuwa kasar faransa kuma a can ne yayi karatunsa .
1046815