IQNA

An Bayyana Iran A Matsayin Daya Daga Cikin Kasashe Masu bada Gudunmawa A Bangaren Kur'ani

22:12 - July 11, 2012
Lambar Labari: 2366533
Bangaren kur'ani, an bayyana jamhuriyar muslunci ta Iran a matsayin daya daga cikin kasashe da suke taka gagarumar rawa a bangarori da daman a ci gaban muslmi a duniya daga ciki kuwa da bangaren yada koyarwar kur'ani mai tsarki ta hanyar shrya taruka da suka danganci littafin mai tsarki.
Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizocewa, an bayyana jamhuriyar muslunci ta Iran a matsayin daya daga cikin kasashe da suke taka gagarumar rawa a bangarori da daman a ci gaban muslmi a duniya daga ciki kuwa da bangaren yada koyarwar kur'ani mai tsarki ta hanyar shrya taruka da suka danganci littafin mai tsarki da haka ya hada shirya gasa a matsayi na kasa d akasa.
Masana dai suna ganin sakamakon yaduwar bukatar komawa ga koyarwar Musulunci a wannan yankin musamman ma a kasar Masar wanda hakan ne ya dawo da mulkin kasar zuwa ga hannun masu kishin Musuluncin sakamakon zaben da aka gudanar, a saboda haka barazanar rugujewa da HKI take fuskanta a halin yanzu tafi ta dukkanin lokutan da suka gabata. A baya dai a lokacin mulkin Hosni Mubarak, kasar Masar ta riki HKI a matsayin abokiyar zama da kuma kulla alaka ta kurkusa da ita, amma a halin yanzu sakamakon dan nasarar da juyin juya halin kasar ya samu ana ganin HKI ne a matsayin abokiyar adawa. Don haka ne ma daya daga cikin bukatun al'ummar Masar shi ne kawo karshen alaka da HKI ta hanyar yin watsi da yarjejeniyar nan ta Camp David.
Su kansu jagororin HKI sun tabbatar da cewa a halin yanzu dai haramtacciyar kasar tana cikin tsaka mai wuya musamman ma bayan nasarar da dan takaran kungiyar Ikhwan al-Muslimi Muhammad Morsi ya samu a zaben shugaban kasar da aka gudanar inda ya zamanto shugaban kasa, to sai dai kuma abin bakin cikin shi ne cewa a daidai lokacin da al'ummomin yankin nan suke kira da kuma kokari wajen ganin gwamnatocinsu kasashensu sun katse duk wata alaka da HKI, a bangare guda kuma sai ga shi wasu gwamnatocin kasashen larabawan irin su Saudiyya da Qatar suna ci gaba da hada baki da HKI da sauran masu goya mata baya na kasashen yammaci wajen ruruta wutar yaki da ayyukan ta'addanci a kasar Siriya da nufin kifar da gwamnatin kasar wacce ta zamanto karfen kafa ga HKI da bakaken aniyarta da na kawayenta a duniyar musulmi.
Ingantattun bayanai suna nuni da hannun da Saudiyya da Qatar da Turkiyya suke da shi wajen ba wa ‘yan ta'adda makaman da suke kai hare-hare kasar Siriyan wanda wasu daga cikin wadannan makaman suna fitowa ne daga HKI. Babbar manufar hakan ita ce kawo karshen wannan gwamnati wacce ta tsaya kyam shekara da shekaru wajen goyon bayan kungiyoyin gwagwarmaya masu adawa da mamayar yahudawan sahyoniya. 1049347

captcha