IQNA

23:45 - July 11, 2012
Lambar Labari: 2366614

An Rera Taken Kasar Tunisia A Wurin Taron Fadakar Musulmi Na Mata

Bangaren kasa da kasa, an rera taken kasar Tunisia a gaban taron fadakar musulmi da ake gudanawar a birnin Tehran tare da halartar masana daga sassa na kasashen duniya musamman daga kasashen musulmi da na larabawa inda mata daga kasar suka taka gagarumar rawa wajen bayyana muhimmancin taron da kuma matsayin fadar musulmi.


Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo cewa, an rera taken kasar Tunisia a gaban taron fadakar musulmi da ake gudanawar a birnin Tehran tare da halartar masana daga sassa na kasashen duniya musamman daga kasashen musulmi da na larabawa inda mata daga kasar suka taka gagarumar rawa wajen bayyana muhimmancin taron da kuma matsayin fadar musulmi da adadinsu ya haura mutane dubu da dari biyu.

A can lardin Qatif da ke gabacin kasar Saudiyya, dubban mutane ne suka gudanar da zanga-zangar nuna kin jinin gidan Sauratar Ali Saud tare kuma da yin kira da a gaggauta samar da sauyi a kasar ta hanyar shimfida salon mulki mai wakiltar al'umma a maimaikon daidaikun mutane 'yayan gidan sarauta da ke sarrafa kasar kamar dai yadda suka ga dama.

Duk da dimbin jami'an tsaron da aka jibge a yankin yau kusan shekara daya kenan, wannan bai hana wa masu zanga-zangar fitowa akan tituna domin yin kira da a sako dukkanin fursunonin siyasa da gidan Sauratar Ali Saud ya bayar da umurnin tsarewa ba.

Tun dai a cikin watan Fabarairun shekarar bara ne mazauna yankin na Qatif da kuma Awamiyya wadanda su ne taskirar dimbin arzikin man fetur da kasar ta mallaka, suka soma gudanar da zanga-zangar lumana domin yin kira da a samar da sauyi a kasar, amma a maimakon sauraren bukatun al'umma, hukumomin kasar sun yanke shawarar ci gaba da yin amfani da karfin wajen murkushe jama'a.

1049535




captcha