IQNA

Juyin Juya Halin Iran Na Da Dangantaka Da Fadakar Musulmi A Duniya

23:45 - July 11, 2012
Lambar Labari: 2366623
Bangaren kasa da kasa, juyin juya halin muslunci day a gudana a jamhuriyar muslunci ta Iran da dangantaka da abin da ke faruwa na fadakar musulmi a halin yanzu a cikin kasashen larabawa musamman inda suke kokarin ficewa daga mulkin mulukiya da zalunci da fir'ananci na sarakunan larabawa da shugabanninsu.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya zanta da daya daga cikin masana masu sharhi day a bayyana cewa, ko shakka babu juyin juya halin muslunci day a gudana a jamhuriyar muslunci ta Iran da dangantaka da abin da ke faruwa na fadakar musulmi a halin yanzu a cikin kasashen larabawa musamman inda suke kokarin ficewa daga mulkin mulukiya da zalunci da fir'ananci na sarakunan larabawa da shugabanninsu yan kama karya.
A nasa bangaren s
Shugaban kasar Iran Dakta Mahmud Ahmadinejad ya bayyana cewar makiyan al'ummomi na asali suna ci gaba da yin dukkanin kokarinsu wajen ganin sun tabbatar da ikon da suke da shi a yankin Gabas ta tsakiya da kuma tseratar da HKI daga hatsarin rugujewa da take fuskanta.
Shugaban na Iran ya bayyana hakan ne a wata ganawar da ya yi da shugaban majalisar kasar Siriya Muhammad Jihad Al-Laham wanda ya kawo ziyarar aiki nan Iran, inda yayin da ya ke bayyana cewar HKI tana hanyar rugujewa gaba daya ne sannan kuma makiyan al'ummar nan suna kokari ne wajen sun tseratar da ita daga wannan matsala da take fuskanta shugaban na Iran ya bayyana rashin jin dadinsa kan yadda wasu gwamnatocin yankin nan suka gafala daga hakan da kuma fadawa tarkon abokan gaba da yaudararsu wai da jin cewa za su iya kare su da tabbatar da su a kan karagar mulki don haka suke ci gaba da kulla alakarsu da HKI.
Har ila yau kuma yayin da ya koma kan abubuwan da ke faruwa a yanki gabas ta tsakiya musamman a kasar Siriya, shugaba Ahmadinejad yace Amurka tana kokarin kare manufofinta ne kawai amma babu abin da ya dame ta da halin da al'ummomi suke ciki, alhali kuwa hakki ne na dukkanin al'ummomi su zaba wa kansu makomarsu, don haka bai kamata su bari wasu su zo daga waje su tsara musu abin da za su yi ba.
Kasashen yammaci dai musamman Amurka suna ganin tsaron HKI na cikin hatsarin gaske sakamakon irin sauye-sauyen da aka samu kuma ake ci gaba da samu a wannan yankin, don haka suke iyakacin kokarinsu wajen su tsamar da HKIn daga wanann hatsari ta kasantuwa da suke fuskanta. Daga cikin hanyoyin da suke bi don cimma wannan manufar sun hada har da kokari wajen mallake wadannan yunkurin neman sauyin da suka kunno kai da kuma kawar da su daga manufofinsu na asali. Hakan ne ma ya sanya su haifar da fitinun da ke faruwa a kasar Siriya da sunan goyon bayan bukatar al'ummar kasar na neman sauyi.
Masana dai suna ganin sakamakon yaduwar bukatar komawa ga koyarwar Musulunci a wannan yankin musamman ma a kasar Masar wanda hakan ne ya dawo da mulkin kasar zuwa ga hannun masu kishin Musuluncin sakamakon zaben da aka gudanar, a saboda haka barazanar rugujewa da HKI take fuskanta a halin yanzu tafi ta dukkanin lokutan da suka gabata. A baya dai a lokacin mulkin Hosni Mubarak, kasar Masar ta riki HKI a matsayin abokiyar zama da kuma kulla alaka ta kurkusa da ita, amma a halin yanzu sakamakon dan nasarar da juyin juya halin kasar ya samu ana ganin HKI ne a matsayin abokiyar adawa. Don haka ne ma daya daga cikin bukatun al'ummar Masar shi ne kawo karshen alaka da HKI ta hanyar yin watsi da yarjejeniyar nan ta Camp David.
Su kansu jagororin HKI sun tabbatar da cewa a halin yanzu dai haramtacciyar kasar tana cikin tsaka mai wuya musamman ma bayan nasarar da dan takaran kungiyar Ikhwan al-Muslimi Muhammad Morsi ya samu a zaben shugaban kasar da aka gudanar inda ya zamanto shugaban kasa.
To sai dai kuma abin bakin cikin shi ne cewa a daidai lokacin da al'ummomin yankin nan suke kira da kuma kokari wajen ganin gwamnatocinsu kasashensu sun katse duk wata alaka da HKI, a bangare guda kuma sai ga shi wasu gwamnatocin kasashen larabawan irin su Saudiyya da Qatar suna ci gaba da hada baki da I da sauran masu goya mata baya na kasashen yammaci wajen ruruta wutar yaki da ayyukan ta'addanci a kasar Siriya da nufin kifar da gwamnatin kasar.
1047901



captcha