Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo cewa, yanzu haka dai an kawo karshen wani taro na bayar da horo kan karatu da hardar kur’ani mai tsarki da aka gudanar a kasar Takistan tare da halartar wakilan makarantun addini musamman masu koyar da karatu da tajwidin karatun kur’ani wato ilimin sanin kaidojinsa wanda aka sab ahudanarwa a kowace a lokacin da ake shirin shiga watan Ramadan mai alfarma.
A wani labari na daban kuma kungiyar kare hakkin bil-Adama ta Amnesty International ta gargadi sabbin mahukuntan kasar Libiya da su kiyayi sake maimaita kuskuren gudanar da mulki kama karya a kasar, kungiyar ta Amnesty International a yau lahadi ta fitar da gargadin cewa; Jami'an gwamnatin Libiya na yanzu da suke kokarin gudanar da zaben 'yan Majalisun Dokokin Kasar a ranar asabar mai zuwa da su tabbatar sun yi tsayin daka wajen ganin sun gudanar da zaben kamar yadda tsarin doka ya shimfida saboda zaben ya kasance karkashin tsarin dimokaradiyya.
Har ila yau kungiyara ta Amnesty International ta bayyana cewa; dole ne a kan mahukuntan kasar ta Libiya su dauki matakin ganin an kawo karshen watsuwar makamai a hannun jama'a, tare da gaggauta gudanar da bincike kan mutanen da ake tsare da su a gidajen kurkuku ba tare da an yi musu shari'a ba.
Kungiyar kare hakkin bil-Adama ta Amnesty International ta kuma gargadi sabbin jami'an Libiya da su kiyayi sake maimaita kuskuren da hambararren shugaban kasar marigayi Mu'ammar Gaddafi ya aikata, ta hanyar gudanar da sabon salon mulkin kama karya a kasar
1050188