IQNA

17:45 - July 13, 2012
Lambar Labari: 2367323

An Kirayi Mahukuntan Bahrain Da Su Gaggauta Sakin Shugaban Kare Hakkin Bil Adama

Bangaren kasa da kasa, kungiyar kare hakkin bil adama ta Amnesty International ta kirayi mahukuntan kasar Bahrain da su gaggauta sakin shugaban kungiyar kare hakkin bil adama ta kasar Nabil Rajab da suke tsare da shi saboda ra’yoyinsa na siyasa inda yake kira da ayi adalci a cikin harkokin mulki da siyasar kasar lamarin da ya bakanta wa mahukunta.

Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Europe cewa kungiyar kare hakkin bil adama ta Amnesty International ta kirayi mahukuntan kasar Bahrain da su gaggauta sakin shugaban kungiyar kare hakkin bil adama ta kasar Nabil Rajab da suke tsare da shi saboda ra’yoyinsa na siyasa inda yake kira da ayi adalci a cikin harkokin mulki da siyasar kasar lamarin da ya bakanta wa mahukunta kasantuwar su ne kan gaba wajen cin zarafin fararen hula.
A wani labarin na daban kuma Gwamnatin kasar Rasha ta nuna matukar damuwa dangane da yadda mahukuntan Saudiyya suke yin amfani da karfifiye da kima wajen murkushe fararen hula masu zanga-zangar a yankunan gabacin kasar.
Babban jami’I mai kula da harkokin kasashen larabawa a ma’aikatar harkokin wajen kasar Rasha Qostine Dolgov ya fadi jiya a gaban manema labarai a birnin Moscow cewa, gwamnatin Saudiyya tana yin amfani da karfi kan fararen hula marassa kariya da suke neman hakkokinsu da aka haramta musu, wanda hakan yay i hannun riga da abin da gwamnatin Saudiyya take raya na neman kare hakkokin bil adama a Syria.
Tun bayan kama babban malamin yankin Awamiyya na gabacin kasar Saudiya a cikin ‘yan kwanakin da suka gabata, yankunan gabacin kasar ke ci gaba da fuskantar boren al’umma, wanda dubban jami’an tsaro ke ci gaba da yin amfani da karfi domin murkushe masu boren.


1051698




captcha