Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na tmpsreel cewa, an bude wani bangare na kungiyar bunkasa harkokin ilimi da al’adu ta majalisar dinkin duniya UNESCO a jami’ar yankin zirin Gaza kamar yadda masu kula da harkokin jami’ar suka sanar ga manema labarai a cikin wannan mako da aka kammala shirin.
Shugabannin kasashen Masar da Tunusiya sun jaddada wajabcin warware matsalar Palasdinu ta hanyar adalci, a taron manema labarai da suka gudanar a yau juma'a a birnin Alkahira na Masar; shugaban kasar Masar Muhammad Mursi da takwaransa na Tunusiya Muhammad Munsif Almarzuki sun bayyana goyon bayansu ga al'ummar Palasdinu tare da jaddada wajabcin daukan dukkanin matakan da suka dace wajen ganin an warware matsalar Palasdinu ta hanyar adalci.
Har ila yau shugabannin kasashen biyu sun bukaci kawo karshen sabanin da ke tsakanin Palasdinawa musamman manyan kungiyoyin Palasdinawa na Hamas da Fatah.
Yanzu haka dai an bude wani bangare na kungiyar bunkasa harkokin ilimi da al’adu ta majalisar dinkin duniya UNESCO a jami’ar yankin zirin Gaza kamar yadda masu kula da harkokin jami’ar suka sanar ga manema labarai a cikin wannan sati da muke ciki.
1051612