IQNA

13:28 - July 15, 2012
Lambar Labari: 2368833

Limaman Juma'a A yankin Awamiyya Sun Nuna Goyon Baya Ga Sheikh Namir

Bangaren kasa da kasa, limaman juma'a yankunan da daman a kasashen larabawa sun nuna goyon bayansu ga sheikh Namir da mahukuntan Saudiyya suka kames hi bisa zarginsa da tunzura jama'a su kyamaci mahukuntan mulkin kama karya da fir'ananci na kasar.


Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na shafin sadarwa na rasid cewa, da dama daga cikin limaman juma'a yankunan da daman a kasashen larabawa sun nuna goyon bayansu ga sheikh Namir da mahukuntan Saudiyya suka kames hi bisa zarginsa da tunzura jama'a su kyamaci mahukuntan mulkin kama karya da fir'ananci na kasar ta Saudiyya da ba ta san labarin wani abu wais hi demokradiyya ba.
A nasa bangare limamin da ya jagoranci sallar juma'a a birnin Tehran ya bayyana cewa; rawar da mace zata taka a gwagwarmaya da ake yi da 'yan mulkin mallaka da shugabanni 'yan kama karya a kasashen duniya tana da gagarumin tasiri.
A hudubar sallar juma'arsa ta yau a babban masallacin birnin Tehran fadar mulkin kasar Iran Hujjatul-Islam Kazim Siddiqi ya tabo batun zaman taron kasa da kasa na mata dangane da fadarkar Musulunci da aka gudanar a birnin Tehran, inda ya jaddada cewar manufar shirya taron ita ce hada kan mata na kasashen musulmi da fahimtar da su irin makirce makircen da makiya ke kitsawa na mai da matsayin mata baya da mai da su marassa kima a duniya.
Hujjatul-Islam Siddiqi ya kara da cewa; shekaru fiye da 100 ke nan makiya suke amfani da duk wata dama wajen shirya makirce makirce kan raba mata musulmi da kimarsu da girman matsayinsu, amma har yanzu hakarsu ba ta kai ga ruwa ba.
Siddiqi ya kuma furta cewar matsayin mata a mahangar kasashen yammaci shi ne wulakanta mace, rashin ganinta da kima ko mutunci, saboda da mata a wannan mahanga sun zame wata hajar biyan bukatu na sha'awa wadda hakan ba karamin take hakkin dan Adam ba ne.

1052328





captcha