IQNA

Musulmin Kasar Bama Na Fuskantar Matsaloli Na Wariya Da Cin Zarafi

11:52 - July 17, 2012
Lambar Labari: 2370744
Bangaren kasa da kasa, mabiya addinin muslunci na kasar Bama suna mawuyacin hali na fuskantar matsaloli na wariya da danniya daga mahukuntan kasar da suke bin tafarkin addinin buda bayan da wasu daga malaman na buda suka iza wutar riki da tsangwama kan musulmin tare da zargin cewa sun bay an asalain kasar ba ne.
Kmafanin dillancin labaran iqna ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na onislam cewa, mabiya addinin muslunci na kasar Bama suna mawuyacin hali na fuskantar matsaloli na wariya da danniya daga mahukuntan kasar da suke bin tafarkin addinin buda bayan da wasu daga malaman na buda suka iza wutar riki da tsangwama kan musulmin tare da zargin cewa sun bay an asalain kasar ba ne domin kuwa acewarsu dubban shekaru da suka gabata ba bu mabiya addinin muslunci a kasar.
Malamin da ya jagoranci sallar juma'a a birnin Tehran ya bayyana cewa; rawar da mace zata taka a gwagwarmaya da ake yi da 'yan mulkin mallaka da shugabanni 'yan kama karya a kasashen duniya tana da gagarumin tasiri.
A hudubar sallar juma'arsa ta yau a babban masallacin birnin Tehran fadar mulkin kasar Iran Hujjatul-Islam Kazim Siddiqi ya tabo batun zaman taron kasa da kasa na mata dangane da fadarkar Musulunci da aka gudanar a birnin Tehran, inda ya jaddada cewar manufar shirya taron ita ce hada kan mata na kasashen musulmi da fahimtar da su irin makirce makircen da makiya ke kitsawa na mai da matsayin mata baya da mai da su marassa kima a duniya.
Hujjatul-Islam Siddiqi ya kara da cewa; shekaru fiye da ke nan makiya suke amfani da duk wata dama wajen shirya makirce makirce kan raba mata musulmi da kimarsu da girman matsayinsu, amma har yanzu hakarsu ba ta kai ga ruwa ba.
Siddiqi ya kuma furta cewar matsayin mata a mahangar kasashen yammaci shi ne wulakanta mace, rashin ganinta da kima ko mutunci, saboda da mata a wannan mahanga sun zame wata hajar biyan bukatu na sha'awa wadda hakan ba karamin take hakkin dan Adam ba ne.

1054450

captcha