Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na baje kolin kur’ani cewa, an nuna wata sabuwar taswira ta hubbaren Imam Ali (AS) a taron baje kolin kur’ani mai tsarki na kasa da kasa da ake gudanarwa yanzu ahaka a birnin Tehran tare da halartar cibiyoyin ilimi da madaba’antu da uke buga litatafai na addinin muslunci musamman wadanda suka dangaci kur’ani mai tsarki kamar dai yadda bangarorin da suke kula shirin suka tabbatar.
Har ila yau kuma yayin da ya koma kan abubuwan da ke faruwa a yanki gabas ta tsakiya musamman a kasar Siriya, shugaba Ahmadinejad yace Amurka tana kokarin kare manufofinta ne kawai amma babu abin da ya dame ta da halin da al'ummomi suke ciki, alhali kuwa hakki ne na dukkanin al'ummomi su zaba wa kansu makomarsu, don haka bai kamata su bari wasu su zo daga waje su tsara musu abin da za su yi ba.
Kasashen yammaci dai musamman Amurka suna ganin tsaron HKI na cikin hatsarin gaske sakamakon irin sauye-sauyen da aka samu kuma ake ci gaba da samu a wannan yankin, don haka suke iyakacin kokarinsu wajen su tsamar da HKIn daga wanann hatsari ta kasantuwa da suke fuskanta. Daga cikin hanyoyin da suke bi don cimma wannan manufar sun hada har da kokari wajen mallake wadannan yunkurin neman sauyin da suka kunno kai da kuma kawar da su daga manufofinsu na asali. Hakan ne ma ya sanya su haifar da fitinun da ke faruwa a kasar Siriya da sunan goyon bayan bukatar al'ummar kasar na neman sauyi.
Masana dai suna ganin sakamakon yaduwar bukatar komawa ga koyarwar Musulunci a wannan yankin musamman ma a kasar Masar wanda hakan ne ya dawo da mulkin kasar zuwa ga hannun masu kishin Musuluncin sakamakon zaben da aka gudanar, a saboda haka barazanar rugujewa da HKI take fuskanta a halin yanzu tafi ta dukkanin lokutan da suka gabata. A baya dai a lokacin mulkin Hosni Mubarak, kasar Masar ta riki HKI a matsayin abokiyar zama da kuma kulla alaka ta kurkusa da ita, amma a halin yanzu sakamakon dan nasarar da juyin juya halin kasar ya samu ana ganin HKI ne a matsayin abokiyar adawa. Don haka ne ma daya daga cikin bukatun al'ummar Masar shi ne kawo karshen alaka da HKI ta hanyar yin watsi da yarjejeniyar nan ta Camp David.
Su kansu jagororin HKI sun tabbatar da cewa a halin yanzu dai haramtacciyar kasar tana cikin tsaka mai wuya musamman ma bayan nasarar da dan takaran kungiyar Ikhwan al-Muslimi Muhammad Morsi ya samu a zaben shugaban kasar da aka gudanar inda ya zamanto shugaban kasa.
1056898