IQNA

An Tura Masu Isar da Sakon Musulunci Zuwa Yankuna Na kasar Pakistan

17:49 - July 21, 2012
Lambar Labari: 2373892
Bangaren siyasa da zamantakewa, an tura masu isar da sakon addinin muslunci a cikin wannan wata na Ramadan mai alfarma zuwa yankuna na kasar Pakistan domin yin wa’azi ga mutane da kuma fadakar da su kamar dai banagarorin da suke daukar shirya tarukan suka sheda.
Kamfanin dilalncin labran iqna ya ahbarat cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo cewa, an tura masu isar da sakon addinin muslunci a cikin wannan wata na Ramadan mai alfarma zuwa yankuna na kasar Pakistan domin yin wa’azi ga mutane da kuma fadakar da su kamar dai banagarorin da suke daukar shirya tarukan suka sheda a cikin kwanakin nan.
An fara gudanar da azumin watan Ramadana a kasashe da dama na duniya a yau juma'a, daga cikin kasashen da aka soma azumin kuwa har da tarayyar Najeriya da kuma jamhuriyar Nijar, A Najeriyar dai Maimartaba sarkin Musulmi Alhaji Sa'ad Abubakar na 3 ne ya tabbatar da cewa an ga watan a jahohi 8 na kasar, yayin da a can jamhuriyar Nijar kuwa Majalisar koli ta harkokin addinin musulunci ce ta tabbatar da ganin watan a yankuna da dama na kasar sannan kuma aka sanar da hakan ta kafafen yada labarai mallakar gwamnati a cikin daren jiya.
Domin magance matsaloli na hauhawar farashin kayayyakin abinci da na masarufi a cikin wannan wata, hukumomi a jamhuriyar Nijar sun ce sun samar da nau'o'in abinci da kuma sukari da za a rika sayar wa jama'ar kasar a kan farashi mai rahusa a duk tsawon wannan wata, inda za a sayar da buhun sukari mai nauyin kg 25 a kan jika 17 da rabi na cfa a maimakon jika 29 da ake sayar da shi a kasuwannin kasar.
1057425




captcha