Bangaren kasa da kasa, an fara sayar da abinci karkashin shirin nan na abincin Halal a kasar Indonesia wnda wani babban otel na kasar da ke yawan masu sayen abincinsa ya fara gudanarwa da nufin jawo hankalin musulmi da suke bukatar abincin halal bisa tsari na zamani domin kaucewa abubuwan da bas u da bukata.
Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo The Jakarta Post cewa, yanzu haka an fara sayar da abinci karkashin shirin nan na abincin Halal a kasar Indonesia wnda wani babban otel na kasar da ke yawan masu sayen abincinsa ya fara gudanarwa da nufin jawo hankalin musulmi da suke bukatar abincin halal bisa tsari na zamani domin kaucewa abubuwan da bas u da bukata.
A kasashen musulmi da dama An fara gudanar da azumin watan Ramadana a kasashe da dama na duniya a yau juma'a, daga cikin kasashen da aka soma azumin kuwa har da tarayyar Najeriya da kuma wasu kasashen a dai Maimartaba sarkin Musulmi Alhaji Sa'ad Abubakar na 3 ne ya tabbatar da cewa an ga watan a jahohi 8 na kasar, yayin da a can jamhuriyar Nijar kuwa Majalisar koli ta harkokin addinin musulunci ce ta tabbatar da ganin watan a yankuna da dama na kasar sannan kuma aka sanar da hakan ta kafafen yada labarai mallakar gwamnati a cikin daren jiya.
Saboda magance matsaloli na hauhawar farashin kayayyakin abinci da na masarufi a cikin wannan wata, hukumomi a jamhuriyar Nijar sun ce sun samar da nau'o'in abinci da kuma sukari da za a rika sayar wa jama'ar kasar a kan farashi mai rahusa a duk tsawon wannan wata, inda za a sayar da buhun sukari mai nauyin kg 25 a kan jika 17 da rabi na cfa a maimakon jika 29 da ake sayar da shi a kasuwannin kasar wadda ta saba da fuskantar matsaloli da dama.
1056850