IQNA

An Sake Yin Dubi Kan Bayanin Jagoran Juyin Juya Hali Kan Kisan Musulmin Myanmar

11:54 - July 22, 2012
Lambar Labari: 2374427
Bangaren siyasa, an sake yin dubi kan wani dadden bayani da jagoran juyin juya halin muslunci ya yi kimanin shekaru ashirin da daya da suka gabata kan kisan gilla da aka yi kan musulmin kasar Myanmar a lokacin wanda akuma halin yanzu lamarin na sake dawowa kamar yadda aka yi ko ma fiye da yadda aka kashe su a lokacin.
Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na bangaren hula da jama’a na ofishin jagoran juyin juya halin muslunci cewa, an sake yin dubi kan wani dadden bayani da jagoran juyin juya halin muslunci ya yi kimanin shekaru ashirin da daya da suka gabata kan kisan gilla da aka yi kan musulmin kasar Myanmar a lokacin wanda akuma halin yanzu lamarin na sake dawowa kamar yadda aka yi ko ma fiye da yadda aka kashe su a lokacin da ya gabata.
A nata bangaren kungiyar Amnesty International mai fafutukan kare hakkokin bil'adama ta bayyana cewar jami'an tsaron gwamnatin Myammar da 'yan kabilar Rakhine suna ci gaba da kai hare-hare da take hakkokin al'ummar musulmi kasar ta hanyar yi musu kisan gilla, fyade da cin mutumci.

A cikin wata sanarwa da kungiyar ta fitar ta bayyana cewar jami'an tsaron suna amfani da karfi a kan musulmin da cin mutumcinsu lamarin da ya ke a matsayin take musu hakkokinsu. Har ila yau kungiyar tace jami'an tsaron suna ci gaba da tsare daruruwan musulmin ba tare da an san inda suke ba.

Kisan gillan da ake yi wa musulmin kasar Myammar din dai ya faro ne tun daga watan Mayun da ya gabata inda daga nan ne ya yadu zuwa yankuna daban-daban. Gwamnatin kasar dai tana ganin wadannan musulmin dai a matsayin wadanda ba 'yan kasa ba.

Cibiyoyi da malamai daban-daban na kasashen musulmi ciki kuwa har da nan Iran suna ci gaba da kiran cibiyoyin kasa da kasa da su dau matakan da suka dace wajen kawo karshen wannan kisan kiyashin da ake yi wa musulman Myammar din.

1058333
captcha