IQNA

13:31 - July 23, 2012
Lambar Labari: 2375529

An Gudanar Da Wani Taro Na Bayar Da Horo Kan Sanin Ilmomin Muslunci A Karachi

Bangaren siyasa, an gudanar da wani taro na bayar da horo ga matasa kan sanin lamurra da suka danganci ilmomin addinin mulunci a birnin Karachi na kasar Pakistan da nufin yin mafani da wannan damar ta lokacin azumin watan Ramadan mai alfarma da mutane suke komawa zuwa lamurra na addini fiye da kowane lokaci.

Kmafanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa cewa an gudanar da wani taro na bayar da horo ga matasa kan sanin lamurra da suka danganci ilmomin addinin mulunci a birnin Karachi na kasar Pakistan da nufin yin mafani da wannan damar ta lokacin azumin watan Ramadan mai alfarma da mutane suke komawa zuwa lamurra na addini fiye da kowane lokaci a cikin kasashen musulmi da na larabawa.
Dangane da batun kisan gilla da cin zarafin da ake yi wa muuslmin da ke makwaftaka da kasar ta Pakistan kuwa, manzon kasar Iran a Majalisar Dinkin Duniya Mohammad Kharzaie ya bukaci babban magatakarda na Majalisar Ban Ki-moon da ya yi amfani da matsayinsa domin kawo karshen kisan kare dangin da ake yi wa al'ummar musulmi a kasar Myanmar.
A cikin wata wasika da ya danka wa Mista Ban Ki-moon a yammacin jiya, manzon na Iran ya ce ce ya kamata ta yi aiki da dokokinta domin kare hakkin dukkanin al'ummomin duniya ba tare da nuna bambanci ba, yana cewa shirun da Majalisar ke yi dangane da korar musulmi da kuma kashe su da ake yi a wannan kasa da ke Asiya wani babban kuskure ne kuma abin zargi.
Yau dai tsawon makwanni biyu kenan da hukumomin kasar ta Myanmar suka bai wa jami'an tsaron kasar izinin soma kwashe musulmin kasar daga garuruwansu na asali, sannan kuma suna rusa masallatai da sauran wurare na ibadarsu amma ba tare da ko kuma kungiyoyin kare hakkokin bil'adama sun ce uffan ba.
1058567


captcha