Bangaren kasa da kasa, kungiyar injiniyoyin kasar Jordan ta fitar da wani bayani da ke yin kakkausar suka da Allawadai da barazanar da yahudawan sahynuiya ke yi kan rusa masallacin Qods mai alfarma tare da yin kira ga sauran kasashen larabawa da na musulmi das u dauki kwararan matakai na hana afkuwar hakan.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga sadarwa na yanar gizo na Palestine cewa, babbar kungiyar injiniyoyin kasar Jordan ta fitar da wani bayani da ke yin kakkausar suka da Allawadai da barazanar da yahudawan sahynuiya ke yi kan rusa masallacin Qods mai alfarma tare da yin kira ga sauran kasashen larabawa da na musulmi das u dauki kwararan matakai na hana afkuwar hakan a yanzu ko kuma nan gaba.
Dangane da shirin na makamashin nukiliya kuwa, kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Ramin Mihmanperast wanda yake gabatar da taron manema labarai a safiyar yau talata a nan birnin Tehran, ya ce Iran za ta ci gaba da taka gagarumar rawa domin bayar da kariyar ga kasuwar man fetur ta duniya.
Kalaman na kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Iran na a matsayin mayar da martani ne ga kasar Amurka wacce ke zargi Iran da kokarin kawo cikas ga kasuwar ta danyan man fetur saboda kasancewar Iran din daya daga cikin kasashen da Allah ya azurta da wannan makamashi. Mihman Perast ya ce a zahiri ma Amurka ce ke neman kawo wa kasuwar mai tarnaki, wannan kuwa ta hanyar sanya takunkumai a kan kamfanonin harkar mai da ke hulda da jamhuriyar Musulunci ta Iran.
Daga karshen kakakin ma'aikatar harkokin wajen ta Iran ya ce kasarsa za ta ci gaba tsayuwa tsayin daka domin hana wa Amurka cimma wannan mummunar manufa tata ta kawo matsaloli a bangaren cinikin man fetur a duniya.
1061471