IQNA

Myanmar ta Zama Ma'auni Na Gane Gaskiyar Masu Da'awar Kare Hakkin Bil Adama

11:06 - July 25, 2012
Lambar Labari: 2377078
Bangaren kasa da kasa, abin da ke faruwa na kisan gilla da kare dangi da ake yi kan mabiya addinin mulsunci a kasar Myanmar ya zama wani ma'auni na gane gaskiyar kasashen da suke raya cewa su suna kare hakkokin bil adama domin kuwa an kashe mutane ta hanyar yankan rago da kone musu gidaje ba tare da irin wadannan kasashen sun ce uffan ba.

Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Aipa cewa, abin da ke faruwa na kisan gilla da kare dangi da ake yi kan mabiya addinin mulsunci a kasar Myanmar ya zama wani ma'auni na gane gaskiyar kasashen da suke raya cewa su suna kare hakkokin bil adama domin kuwa an kashe mutane ta hanyar yankan rago da kone musu gidaje ba tare da irin wadannan kasashen sun ce komai kan lamarin ba.

Shi kuwa shugaban kasar Madagaska Andry Rajoelina ya isa tsibirin seycheller a yau litinin inda ake saran zai gana da abokin hamayyarsa Mark Ravalomanan tsohon shugaban kasar wanda ya ture daga kujerar shugabancin kasar, kamfanin dillancin labaran AFP ya kara da cewa, a gobe talata ne ake saran Mark Ravalomanana zai isa tsibirin na seycheller daga kasar Afrika ta kugu inda yake gudun hijira tun lokacinda aka gwace mulki a hannunsa.

Kungiyar bunkasa tattalin arzikin kasashe kudancin Afirka ta kuduri anniyar kawo mutanen guda biyu gaba da gaba don su warware sabanin da ke tsakaninsu. Wanda hakan zai bada damar gudanar da zabubbuka a kasar ta Madagaska nan gaba.

Kungiyar SADC mai kasashen 15 dai, ta sanya karshen wannan watan yuli ya zama dama ta karshe ga mutanen biyu na su kawo karshen sabanin da ke tsakaninsu wanda ya hana ruwa gudu a harkokin siyasar kasar Madagaska.

1061354

















captcha