Bangaren kasa da kasa, kungiyar hizbullah ta kasar Lebanon ta yi kakausar suka da yin Allawadai da matakan da haramtacciyar kasar Isra’ila ta ke dauka na rusa wurare masu tsarki a cikin yankunan palastinawa musammama birnin Qods mai alfarma.
Kamfanin dilalncin labaran iqna ya ahbarat cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo cewa, kungiyar hizbullah ta kasar Lebanon ta yi kakausar suka da yin Allawadai da matakan da haramtacciyar kasar Isra’ila ta ke dauka na rusa wurare masu tsarki a cikin yankunan palastinawa musammama birnin Qods mai alfarma tun tsawon shekaru da suka gabata har zuwa yau.
A bangare guda kuma shugaban kungiyar Hizbullah ta kasar Labanon Sayyid Hasan Nasrallah ya bayyana cewar a halin yanzu kungiyar ta su (da sauran masu adawa da mulkin mallakan ma'abota girman kai) suna fuskantar wani sabon salo ne na yaki ne wanda Amurka da HKI suke jagorancinsa.
Shugaban na Hizbullah ya bayyana hakan ne a yammacin jiya a lokacin da ya ke gabatar da jawabi a wajen bikin yaye dalibai 'ya'yan shahidan gwagwarmaya ta Musulunci a birnin Beirut na kasar Labanon inda yace sakamakon gazawar da makiya suka yi na mamaya don haka suka koma wajen lalata irin tunanin al'umma don kada a sami jaruman mutane masu tsayin daka. Sayyid Nasrallah ya ci gaba da cewa a halin yanzu makiyan suna amfani da tashohin talabijin don gurbata tunanin al'umma da kuma yada muggan kwayoyi da lalata a tsakanin mutane duk dai da nufin gurbata musu tunani.
Sayyid Nasrallah ya yi watsi da maganganun da wasu suke yadawa na cewa kungiyar ta yi rauni sannan kuma tana fuskantar matsaloli daban-daban yana mai cewa masu wannan tunani suna bayyanar da halin da suke ciki ne. Sayyid Nasrallah ya ja kunnen wadannan mutanen da cewa dogaro da Allah da suke da shi yana kara musu karfi da kuma hakuri komai tsananin wahalar da suka shiga kuwa.
1061887