Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na french.moqawama, cewa kungigyar gwagwarmaya ta hizbullah ta mayar da martani kan zargin da wasu masu tsananin adawa da ita suka yi kan cewa tana da hannu wajen yunkurin yin kisan gilla kan daya daga cikin yan majalisar dokokin kasar daga bangaren sha hudu ga watan Maris Botris Harb, wanda shi kansa ne ya kirkiro zargin kuma ya dora abokansa na siyasa a kansa.
A nasa bangaren jakadan jamhuriyar muslunci ta Iran a kasar Lebanon ya bayyana cewa babbar manufar yahudawan sahyuniya ita ce su ga sun raba al’ummar palastine da dukkanin hakkokinsu tare da mayar da su ‘yan gudun hijira baki daya kamar dai yadda ake gani a halin yanzu.
Babbar kungiyar kasashen musulmi ta yi kakkausar suka da yin Allawadai da haramtacciyar kasar Isra’ila kan harin ta’addancin da ta kai masallatan musulmi palastina a cikin yankunan gabar yamma da kogin Jordan, kmar yadda kuma kasashen larabawa da suke babatun kare hakkokin palastinawa suka gum da bakunansu kan wannan batu.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya naklato daga shafin sadrawa na yanar gizo na CPI cewa, kungiyar kasashen musulmi ta yi kakkausar suka da yin Allawadai da haramtacciyar kasar Isra’ila kan harin ta’addancin da ta kai masallatan musulmi palastina a cikin yankunan gabar yamma da kogin Jordan a cikin wannan mako.
1062343