Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, yua nakalto daga bangaren yada labaransa na cikin gida cewa an nuna wasu daga cikin kayan zane masu kayatarwa da masana kan harkokin fannin zane na addini suka yi a wajen taron babban baje kolin kur’ani mai tsarki na duniya da yanzu haka yake gudana a fadar mulkin jahuriyar muslunci, tare da halartawa masana da wakilan cibiyoyin muslunci na kasashen musulmi har da na larabawa.
A wani labarin kuma an kafa wata sabuwar jam’iyyar musulunci ta kurdawa mai suna jamiyarr muslunci ta Kurdustan kamar yadda wani daya daga cikin fitattun ‘yan siyasa daga ‘yan kabilar Kurdawa na kasar Turkiya ya fada a cikin wani jawabi da ya fitar da sunan jam’iyyar.
A bangare guda kuma a wani labarin na daban, ma’aikatar kula da harkokin muslunci ta kasar Syria ta sanar cewa ta dauki nauyin rubutawa tare da buga wani kwafin kur’ani mai tsarki mai tsarki wanda shi ne irinsa na farko a kasar da nufin kara fito da matsayin kur’ani a kasar wadda daya ce daga cikin kasashen musulmi da sukee taka gagarumar rawa wajen yada addinin musulunci.
Bayanin ya ci gab ada cewa wannan kur’ani na daga cikin muhimman ayyukan da wannan ma’aikata ta gudanar a cikin tarihinta, domin kuwa za a mayar da shi ta wata hanya da dukaknin muslumin kasar za su iya amfana da shi ta hanyoyi masu sauki, kamar saka shi a cikin na’urori na musamman da suke aiki da na’ura mai kwakwalwa, ta yadda za aiya karantawa da sauraren sauti.
Ma’aikatar kula da harkokin muslunci ta kasar Syria ta sanar cewa ta dauki nauyin rubutawa tare da buga wani kwafin kur’ani mai tsarki mai tsarki wanda shi ne irinsa na farko a kasar da nufin kara fito da matsayin kur’ani a kasar wadda a koda yaushe take kokaein ta samar da hanyoyin bunkasa fahimtar musulunci.
1068772